Home / Labarai / Sanata Bello Mandiya Ya Jajantawa Al’umma

Sanata Bello Mandiya Ya Jajantawa Al’umma

Imrana Abdullahi
Sanata Bello Mandiya wakilin yankin Funtuwa da ake kira (Funtuwa Zone) a cikin Jihar katsina ya jajantawa al’umma tare da jan hankali a cikin yanayin da aka samu kai a ciki tun daga matsalar cutar Covid-19 da ake kira Korona da kuma masu satar jama’a domin neman kudin fansa da matsalar masu satar dabbobi da dai halin da ake ciki baki daya, ya dai yi wannan jan hankali ne a cikin shafinsa na Facebook, ga dai abin da ya ce.
Al ummah Funtua zone muma muna cikin damuwa musamman kan matsalar tsaro da covid-19 da wannan nake jajanta mana baki daya Allah yaji kan Wanda suka rasa rayukansu,Allah ya bamu mafita ya kawo karshen halin dardar da ake ciki musamman faskari-Kankara-Dandume da sauransu.
Bisa bincike gwamnatin jahar katsina tana kokari akan sha’anin tsaro.Duk da haka bazamuyi kasa agwiwaba wajen ganin ankawo karshen matsalar tsaro zamu bada shawar-wari da yin duk mai yuwa wajen ganin an cima nasara al ummah ta sami kwanciyar hankali.
Duk da kalu bale da muke fuskanta na hutun dole sakamakon corona virus komi ya tsaya amma abin da yake tilas dole a tunkareshi musamman abin da ya shafi rayuka da dukiyoyin al’ ummah,a karshe muna bada hakuri ga al’ ummah bisa abin da suke gani yana faruwa gwamnati na iya bakin kokarinta akan sha’anin tsaro da sashin lafiya al amarin ne ya wuce duk tunanin mai tunani da ace agaban mutum ake daukar duk irin matakan da ake dauka yana kallo to lallai mutum zai sha mamaki ko shakka babu sai mutum ya yabawa gwamnati.
 komi ya yi tsanani zai zo karshe a kara hakuri kuma abi da addu’a insha Allahu komi zai zama tarihi ,Allah yayimana maganin matsalolinmu da na al’ummar mu ya yi mana jagora.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.