Home / Labarai / Sanata Katung Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Gidan Cocin Katolika A Fadar Kamantan

Sanata Katung Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Gidan Cocin Katolika A Fadar Kamantan

Sanata mai wakiltar yankin Kaduna ta Kudu Sunday Marshal Katung (PDP-Kaduna ta Kudu) ya yi Allah wadai da harin da aka kai gidan limamin cocin Katolika da ke Fadan Kamanton a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kai farmaki gidan limamin cocin, Rabaran.Fr.  Emmanuel Okolo a ranar Alhamis da daddare kuma an kona daukacin Rectory, inda aka kona wani malami mai suna Na’aman Danladi.
A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, Sanata Katung, ya lura cewa, bai kamata a taba barin irin wannan ta’addancin ya ci gaba ba.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kai wani samame na tsawon wata daya a dazuzzukan Kudancin Kaduna da kewaye domin murkushe ‘yan bindigar.

Dan majalisar sai ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin da daukacin al’umma mabiya darikar Katolika a yankin.

“Na ji bakin ciki da wannan labari.  Abin ma ya fi bacin rai cewa sharri ya sake ziyartar al’ummarmu masu zaman lafiya”.

“ A don haka Ina Allah wadai da wannan mummunan harin ta’addanci da ya salwantar da rayuwar matashin malamin mu.

“Kada ta’addanci da cin zarafin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba ba za su taba zama hujja ba ko kuma su kasance cikin abubuwan da ke faruwa a kullum ba”.

“Bai kamata a bari a ci gaba da kai hari irin na matsorata da rashin tausayi ga al’ummarmu ba.

“Tunanina yana tare da dangin wadanda abin ya shafa, abokai, da daukacin al’ummar Katolika a yankin gundumar Kaduna ta Kudu.

“Sakamakon ta’addancin da ‘yan bindiga ke yi a hanyar Kaduna zuwa Kachia, cin zarafi ne kai tsaye ga gwamnatin tarayya da ma hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa “Kuma wannan lokaci ne da za a kai yaki ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a ko’ina suke”.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.