Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da suke fitowa daga Jihar Kaduna na cewa wadansu mutanen da suke cikin Jirgin kasa daga garin Kaduna zuwa Abuja sun tsallake rijiya da baya sakamakon tashin wani abin fashewa da ake zargin cewa Bam ne da wasu yan Ta’adda suka tayar.
Sanata Shehu Sani tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta tsakiya, ya tsallake rijiya da baya a ranar Alhamis lokacin da yake cikin Jirgin kasa daga garin Kaduna zuwa Abuja.
Sanata Sani ya ce Jirgin da yake ciki ya samu matsalar lalacewar wani bangare nasa sakamakon harin da yan Ta’adda suka kai masa da abin fashewa a ranar Laraba.
A shafinsa na tuwita, tsohon dan majalisar Dattawan ya zargi yan Ta’adda da kai harin ta hanyar yin amfani da abin fashewa.
Ya zargi cewa yan ta’addan sun kuma budewa injin din Jirgin wuta da kuma tankin jirgin.
a jiya, yan Ta’adda sun kaiwa Jirgin kasa hari da ke kokarin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja hari da abin fashewa sun kuma budewa injin din wuta inda sun dai- dai injin din da kuma tankin jirgin
“Da safiyar nan kuma sai muka samu kanmu a harin Jirgi inda ya lalata hanyar Jirgin, mun dai samu kan mu ne a matsayin wadanda suka tsallake rijiya da baya kawai”, inji Shehu Sani, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na tuwita.