Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Sanatan da ke wakiltar mazabar shiyyar Kaduna ta uku Sanata Sunday Marshall Katung, ya gabatar da wani kudiri a gaban majalisar Dattawa ta Goma da ke bukatar a kaiwa al’ummar Kudancin Jihar Kaduna dauki game da cutar Diphtheria da ta Bulla a yankin.
Kamar dai yadda aka Sani tun kwanan baya Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa hakika cutar ta Bulla a yankin kuma ta na yin sanadiyyar mutuwar jama’a don haka Gwamna Sanata Uba Sani ya bayar da umarnin gaggawa domin a kai kwararru yankin
Kamar yadda Sanata Sunday Marshall Katung ya gabatar wa majalisar ya ce babu ko shakka cutar na yin sanadiyyar aikawa da jama’a lahira kuma ta na yaduwa a halin yanzu don haka ana bukatar samun taimaki cikin gaggawa daga majalisar
Katung a cikin wata rubutacviyar takardar da ya Gabatarwa majalisar Dattawa ya ce tun biyo bayan rahoton rashin lafiyar wani Yaro mai shekaru hudu da rashin lafiya ta kama shi tun a ranar 4 ga watan Yuli a karamar hukumar Jema’a
Sai kuma aka lura cewa ana samun Barkewar cutar ta Diphtheria da ke daurin kisan mutane kuma ta na daurin yaduwa kwarai a sassan Jihar Kaduna.
An ci gaba da lura da cewa, tun bayan wannan lamari, gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Amai da gudawa a jihar ya kai 17 tare da gano wasu mutane 68 da ake zargin sun kamu da cutar a fadin jihar kamar yadda a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli 2023.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa mutane 10 ne suka mutu sakamakon cutar a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, yayin da yara 3 suka mutu a karamar hukumar Makarfi, ssi kuma wasu bakwai ke kwance a asibiti.
Sanin cewa diphtheria cuta ce mai saurin yaduwa da kwayar cuta mai suna Corynebacterium diphtheria ke haifar wa da masu kamuwa da cutar da matsananciyar matsalar numfashi da hadiyewar matsalolin da ka iya tasowa a fata.
Damuwa da cewa yanayin cutar mai saurin yaduwa yana nufin idan ba tare da gaggawar kokarin dakile ta ba, cutar za ta yadu cikin mummunan yanayi musamman idan aka yi la’akari da yanayin rayuwa da zamantakewar al’umma a mafi yawan yankunan karkara a Najeriya.
Domin irin yadda abubuwan da Najeriya ta samu kwanan nan game da kwayar cutar Ebola da kuma cutar ta Cutar Korona ya nuna dalilin da ya sa dole ne a yaki barkewar cutar tare da mafi kyawun kayan aikin likitanci da kimiyya da ilimin da ake da su.
Ya bukaci majalisar dattijai da ta umarci ma’aikatar lafiya ta tarayya da cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya da su hada kai da manyan ma’aikatar lafiya ta Jihar Kaduna wajen kara kaimi wajen neman masu kamuwa da cutar diphtheria tare da gano wa ta hanyar tuntuɓar juna, ayyukan sadarwar da sauran dukkan hanyoyin da suka dace abi domin kwalliya ta biya kudi sabulu.
Ya bukaci majalisar dattijai da ta baiwa ma’aikatar lafiya ta tarayya damar yin cudanya da ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna da nufin kai ma’aikatan lafiya yankunan da abin ya shafa da kuma kara kaimi wajen sa ido a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, ya bukaci majalisar dattijai da ta sake yin wasu umarni kamar yadda ake ganin ya dace a cikin yanayi.