Home / KUNGIYOYI / Sardaunan Badarawa Ya Kaddamar Da Littafin Jam’iyyar Matan Arewa Da Naira Dubu Dari Bakwai (700,000)
This is the Sardaunan Badarawa

Sardaunan Badarawa Ya Kaddamar Da Littafin Jam’iyyar Matan Arewa Da Naira Dubu Dari Bakwai (700,000)

Daga Imrana Abdullahi

Honarabul Usman Ibrahim Sardaunan Badarawa, Santurakin Hausa kuma Garkuwan Matasan Najeriya, a kokarinsa na ganin ya taimakawa kungiyoyin da suke gudanar da ayyuka domin ci gaban al’umma musamman marasa galihu ya kaddamar  da littafin Jam’iyyar matan Arewa reshen Jihar Kaduna da tsabar kudi naira dubu dari Bakwai domin su samu sukunin ci gaba da aiwatar da ayyukansu na taimakawa mata da daukacin al’umma baki daya.

Honarabul Ado Lawal Dankoli, ne ya sanar da wannan kyautar kudi kuma ya bayar da su nan take a lokacin da ya wakilci Sardaunan Badarawa a wajen babban taron kungiyar jam’iyyar Matan Arewa reshen Jihar Kaduna da aka yi a dakin taro na gudan tunawa da marigayi Sa Ahmadu Bello.

Honarabul Ado Dankoli, ya ci gaba da bayanin cewa
“Hakika wannan kungiya ce mai Dogon tarihi, wanda a da can Kunyi Bacci kadan amma koda yake a yanzu Allah yasa kun fara don haka abu ne mai kyau da zai amfani jama’a Maza da Mata, Yara Da Manya.

Dankoli ya kara da cewa “Babu shugabanci, ko Gida da za a zauna lafiya ba tare da cikakkiyar gudunmawar mata ba”.

Wadansu abubuwa na gudana tare da daukacin mata, masu mulki duk inda mutum yaje zai koma ga matan ne su bashi abinci da dai sauran hidindumun da dace a yi wa mutum,Malami ne, masu Sarauta duk mata na da damar juya lamarin su a cikin gida ko yaya ne da dai duk wani mutum a cikin al’umma, ina fata zaku yi kokarin yada wannan ayyukan na ku zuwa kauyuka domin ana bukatarsu kwarai.

“Sardauna na son rike wannan kungiya ya bata goyon bayan da ya dace domin a ta fi tare

Da suke gabatar da jawabi a wajen taron daukacin wadanda suka yi jawabai da suka hada da Maza da mata duk sun yi bayani a kan bukatar samun hadin kai a tsakanin mata wanda idan an samu hakan za a samu ci gaban da ya dace al’umma su samu.

Sai kuma ainihin jawaban da yayan kungiyar jam’iyyar Matan Arewa suka gabatar sun ce za su ci gaba da kokarin ganin sun horas da matan birni da na karkara a kowa ne lungu da sako na Jihar Kaduna da sana’o’i da kuma sauran al’amuran ilimi da sauran fannonin ciyar da rayuwar bil’adama gaba.

An kuma bayyana sunayen wadansu muhimman mutane da suka kawo ci gaban kasa a wajen taron

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.