A ranar 29 ga watan Mayu ne Gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu Sakkwato, ya cika shekara daya a kan karagar mulkin Jihar. Ya kuma ba kansa babban maki na Yabo da cewa Gwamnatinsa ta yi rawar gani a cikin shekarar daya.
A cikin wannan makala ko rubutun, mun yi bitar abubuwan da suka faru da aka aikata karkashin jagorancinsa musamman a kan harkar tsaro wanda kuma shi ne abu na farko a cikin jerin ajandodinsa guda Tara (9) da kuma batun biyan kudin ajiye aiki ko kammala aiki na ma’aikatan Jihar da suka yi ritaya a Jihar.
A lokacin Yakin neman zabe na shekarar 2023 na jam’iyyar APCwad da ya yi takarar gwamna a karkashin ta, an ga Ahmed Aliyu Sakkwato a kowane lokaci da jam’iyyar APC ta fita gangamin yakin neman zabe, ya na yin rantsuwar cewa zai kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar Jahar. Musamman ma a bangaren Sakkwato ta Gabs, kuma ya na ikirarin cewa zai biya kudi ajiye aiki na ma’aikatan Jahar, zai kuma samar da ababen more rayuwa a kowane lungu da sako na jihar da dai sauran alkawura da dama.
2. A yanzu shekara daya, Gwamna Ahmed Aliyu ya kasa cika alkawarinsa da ya yi wa jama’a, maimakon hakan, sai dai kawai jama’ar Jihar na Jin Gwamna Ahmed Aliyu na kokarin Dora laifi ga Gwamnatin da ta wuce karkashin jagorancin tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal cewa baiyi kaza ba ko bai yi kaza da kaza ba, kamar dai har yanzu Aminu ne Gwamna yayinda shi Ahmed yake neman goyon bayan jama’a wajen ganin ya ci zabe. A sakamakon hakan ne muke ganin ya dace Gwamna Ahmed Aliyu ya daina Dora laifi ga kowa ya koma kawai ya fuskanci kalubalen cika alkawarin da ya yi na bukatun al’ummar Jahar Sakkwato .
3. A cikin abubuwa masu muhimmanci ga alkawulan da Gwamnan ya yi a lokacin Yakin meman Zabe cewa zai yi amfani da kudin Jahar koda zasu kare domin ya kawo karshen matsalar tsaro . Amma a halin yanzu matsalar tsaro a Jahar tun lokacin da aka Rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 lamarin matsalar tsaro ta kara tabarbarewa ne kawai, inda ko dai an kashe jama’a ko an sace su ko kuma an barsu a cikin wani mawuyacin hali ana yi wa Mata fade da kuma biyan makudan kudi a matsayin fansa ga yan Ta’adda masu shan jinin jama’a da ake yi wa lakabi da yan bindiga.
4. Daga shekarar 2019 da yan Ta’adda suka fara yin amfani da miyagun makamai ga al’ummar Tabanni a karamar hukumar Raba, Dan tasakko a karamar hukumar Gwaranyo, Garki a karamar hukumar Sabon Birni da kuma kisan da aka yi wa jama’a a ranar Lahadi a kasuwar Goronyo ,babu wani lokaci ko sau daya da Jagororin jam’iyar APC a Jihar Sakkwato suka kai ziyara ko ya jajantawa wadanda lamarin ya shafa na rasa al’ummarsu.
A lokacin duk mun yi tsammanin cewa suna son yin amfani da batun kasha- kashe ne don su dogara da shi su tabbatar da sun samu mulki, amma ba wanda ya yi tsammani gwannatin APC za ta ci gaba da yin halin ko-in kula game da batun rasa rayuka, dukiya da ake yi musamman ga mutanen shiyyar Sakkwato ta Gabas ko kuma a ko’ina a duk fadin Jahar musamman idan aka yi la’akari da rashin jajantawa da suke yi ga al’ummar da abin ya shafa.Tun lokacin da suka samu mulki in banda ziyarar da gwamna ya ya kai Giyawa da Tangaza a kananan hukumomin Goronyo da Tangaza inda ya jajantawa mutanen da abin ya shafa sakamakon irin harin da yan bindiga suka kai masu babu wata ziyarar jaje ko tallafi da ya sake kaiwa ko bayarwa ga wadanda iftila’in matsalarn tsaro ke shafa.kuma ko waccan ziyarar da ya kai sai da aka yi ta suka da ce-ce-kuce kan rashin halin ko’inkula da yake nunawa sannan ya kai ziyarar.
5. Hakika ya na nan cikin tarihi cewa Gwamna Tambuwal a koda yaushe ya na soke duk abin da yake yi a ko’ina yake a duk fadin duniya ya kuma dawo Sakkwato domin jajantawa duk wasu al’ummar da suka Sami kansu cikin harin yan bindiga. A wasu lokutan saboda takaici da ke kama shi sai dai ya rika zubar da Hawkeye kawai idan ya ga Gawar da aka kashe ta mutane ba gaira ba dalili; Gaskiya ne wani lokacin ma ya na yin kuka a game da irin mutanen da aka kashe ko halin da ake ciki domin ya kasa hana faruwar hakan sakamakon bashi keda iko da jami’an tsaro ba.
6. A halin yanzu a hedikwatar karamar hukumar Isa a cike take da yan gudun hijira da suka fito daga garuruwan Tidibale, Gidan Sale, Gidan Rana, Girnashe da sauran wurare da dama da tuni an kashe wadansu mutane da dama an kuma sace wadansu tare da sace dabbobinsun an kuma Kone gidajensu ko wurin da suke zama sakamakon aikin yan bindiga.Haka lamarin yake a karamar hukumar Sabon Birni da a wuraren garuruwa irinsu Gatawa, Gangara, Kagara, Tarah, Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamna na yanzu, Makwaruwa, Lajinge da sauran wurare da yawa ana kai wa wuraren hari a duk rana ta Allah kuma masu wannan aikin kai wa jama’a hare – haren na yawo ko’ina a duk lokacin da suke bukata ba tare da samun wata matsala ba, suna kashe mutane suna satar wadanda suke bukata da suka hada da mata domin biyan bukatarsu suna kuma Dorawa jama’a haraji in har suna son su Noma Gonakinsu.Ya zuwa lokacin rubuta wannan sharhi abin da Jihar Sakkwatonke ciki, sahihan bayanai na cewa wasu kauyuka a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni tuni yan bindiga sun tashe su baki daya saboda haka babu wadansu mutanen da suke zaune a wurin, wato dai kauyukan sun koma Kufai kenan.
Kuma yan bindigan sun Sanya makudan miliyoyin a matsayin kudin harajin da zai ba su damar su dawo garuruwansu duk da cewa mutanen sun zama yan gudun hijira a inda suke don haka idan suna son komawa Gonakinsu ma yanzu haka sai sun biya wadannan makudan miliyoyin naira tukunna, Kauyukan sun hada da Tashar Bagaruwa, Gidan Auta, Teke mai kasuwa, Tashar Ango, Teke mai Fuloti, Gidan Alewa, Kuka Majema, Kuka Tudu, Kuka, Inwala, Gidan Ayya, Santar Dan Hillo, Hawan Diram da Dakwaro, duk sun gamu da jarabawar matsalar son zuciyar yan bindiga.
7. Kamar Jihohin Katsina da Zamfara, Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya samar da rundunar tsaron yan sa kai, amma abin mamaki tun bayan da suka kammala samun horo, shi ne Gwamna guda tilo cikin wadannan gwannoni da bai ba wadannan ‘yan sakai koda Sanda ba da za su yi amfani da ita wajen harkar tsaron jama’a da dukiyoyinsu. Don haka za a iya cewa su wadannan jami’an tsaron sa kai da Gwamnatin jihar Sakkwato ta samar ne mafi samun koma baya idan aka yi la’akari da rashin samun kayan aiki.Wanda hakan na nufin kenan masu aikin tsaron Sa kan za su iya zama cikin hadarin salwantar rayukansu daga matsalar yan bindiga a duk lokacin da suka kai wa wadansu mutane hari.
Muna so mai karatu ya sani , hatta da irin Baburan hawan da aka nuna a wajen taron kaddamar da wadannan ‘yan sa kai ba a raba su ba ga masu aikin Sa kan. Abin tambaya anan shine, ko dai an yi hayar Baburan ne domin kawai ayi taron kuma an mayar wa masu shi tun bayan kammala taron? Abin lura anan shine, Gwanbatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Ahmed Aliyu Sakkwato ba ta yi komai ba kenan domin yin maganin yan bindiga da duk wata matsalar tsaron lafiya da dukiyar jama’a da Jihar ke fama da ita.Kuma ba a yi komai ba domin a taimaka wa dimbin yan gudun hijirar da suka rasa muhallinsu suka koma sansanin yan gudun hijira wadanda da yawa daga cikinsu ke yawo a kan titunan babban birnin Jahar suna barace- barace domin samun abin da za su Sanya a bakin salati a kalla su ciyar da kansu.
8. A bangaren Ma’aikata musamman yan fansho da suke jiran a biya su kudin ajiye aiki ana ta yi masu romon baka kawai cewa in dai an zabi jam’iyyar APC ta Dare madafun iko za a samu wani abu tamkar saukake daga sama cewa dukkan matsalolinsu za a warware su duk baki daya. Amma sai gashi abu guda daya kawai da Gwamnatin Ahmed Aliyu ta yi a zamanin shekarar farko shi ne na kafa kwamiti domin ya bincika ya gano tare da samar da wani sahihi ko sahihan alkalumma na yawan ma’aikatan da suka ajiye aiki da suke bin Gwannatin Jihar kudin ariyas. Kuma an ba kwamitin ne sati biyu domin ya gabatar da rahotonsa amma sai ya dauki watanni kafin ya gabatar rahoton da aikin da aka bashi
9. A cikin rahoton,Sun tabbatar da samun masu jiran a biyasu kudinsu da suka kai mutane dubu 4000 kuma mutane dari Tara (900) daga cikinsu duk sun rasa rayukkansu, dukkansu masu rai da matatun suna jiran a biya su kudi a kalla naira biliyan 14, da suke bin Gwannatin jihar Sakkwato bashi na kudin ajiye aiki da kuma hakkin wadanda suka ajiye aikin ba a biya su ba har suka mutu suna cikin jira. Hakika a nan ya kasance cewa ba a iya kawar da kokarin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi na a lokacin Mulkinsa ya biya makudan miliyoyin kudi ga wadanda suke da hakki bayan barinsu aiki musamman na biyan kudin fansho a lokacin da ya dace. Amma abin mamaki sai ga shi duk da irin makudan kudin da suke shigowa daga Gwamnatin tarayya a wata wata a halin yanzu kuma ga alkawarin da Gwamnan ya yi na biyan bashin wadanda suka ajiye aikin, Gwamna yace zai ajiye kudi a kalla naira biliyan biyar domin kaddamar da biyan kudin wadanda ke ta jira bayan sun ajiye aiki da za a biya kudinsu har ma da wadanda suka rasu ba a biya su ba wanda a halin yanzu iyalansu ke jira a biya su kudin.
10. Abin bakin ciki, shi ne rayuwar wadannan ma’aikatan da suka yi ritaya ta kara shiga cikin kunci da bakin ciki a lokacin da suka samu labarin cewa Gwamnan ya ware kudi naira miliyan dari biyar (500) a duk wata domin biyan bashin da suke bi, inda ya kaddamarda soma biyan kudin a ranar 29 ga watan Mayu, 2024. Saboda haka abin da lamarin ke nufi shi ne wadansu da suka ajiye aikin za su ci gaba da jira har sai nan da shekarar 2026 kenan kafin a biya su kudinsu, saboda idan dai naira biliyan 14 an raba ta da naira miliyan dari biyar a kowane wata, zai dauki a kalla watanni 28 ko kuma shekaru biyu da watanni hudu kafin a kammala biyansu kudin hakkin su na ariyas. Kuma wani batu mara dadin ji ga wadanda suka ajiye aikin kuma shi ne daga watan Mayu 2024 zuwa 2026 in an kammala biyansu ,nan ma wadansu tarin ma’aikata masu jiran a biya su Hakkinsu zai kara taruwa.
11. A jihohi makwabta kamar Zamfara da Gwamna Dauda Lawal ke yi wa shugabanci ya ware naira biliyan hudu domin ya biya dukkan bashin wadanda suka ajiye aiki, jihar Borno Gwamna Babagana Zulum, shima yayi kwatankwacin wannan kokarin inda ya biya wadanda suka ajiye aiki daga shekarar 2011zuwa 2024 . Amma mutum zai rika mamakin cewa me yasa Ahmed Aliyu ya zabi ya fara biyan kudin da kudi masu kankata na naira miliyan dari biyar (500) a wata duk da cewa an samu karin kudin shiga daga Gwamnatin tarayya da Jahar Sakkwato ke samu da kashi dari tun daga watan Yuni 2023.
12. Gwamnan dai kamar yadda aka saba ya na ta Dora laifi tare da suka ga wanda ya gada wato Aminu Waziri Tambuwal a game da rashin biyan kudi ma’aikatan da suka ajiye aiki. Ya manta ko kuma da gangan baya son ganin laifin ubangidansa, Aliyu Magatakarda Wamakko wanda shine silar taruwar wannan bashin na wanda suka yi ritaya ta hanyar kin biyan kudin fansho da garatuti duk da cewa bai samu wata matsalar kudin yan fansho da gratiti ba a Jihar Sakkwato a lokacin da ya samu damar Dare ragamar mulkin Jihar Sakkwato daga hannun Alhaji Attahiru DalhatuBafarawa.
13. Hakika ya na cikin kundin tarihi cewa Gwamna Wamakko bai biya kudin da ya dace ya biya na sauran Gwamnonin da suka gabace shi ba bale kuma na ma’aikatanda suka ajiye aiki ba wanda hakan ya Jefa dimbin al’umma cikin matsalolin rayuwa da dama kuma dole sai da mutane suka yi ta jira tsawon shekaru bayan sun kammala aikin Gwamnati suna jiran ranar da za a biya su.
14. Zamanin mulkin Gwamna Aminu, kamar na dukkan sauran yan uwansa zababbu da aka zabe su a lokaci guda duk sun fara ne a cikin yanayi na rashin dadi musamman game da al’amuran da suka shafi kudi wanda sakamakon hakan ne Gwamnatin tarayya ta ba su wadansu kudin ceto da ake kira da belout domin su samu sukunin fara wa daga farko. Jihar Sakkwato kuma ta samu kudi naira biliyan hudu (4) domin biyan kudin ariyas. An kuma Sanya kwamiti karkashin shugabancin wanda a yanzu shi ne babban akanta janar na jahar Sakkwato a yanzu, Umaru Ahmed Tambiwal, domin su tantance su kuma fitar da ainihin sahihin sunaye mutanen da suke bin Gwannatin Jiha bashin kudin na ajiye aiki,ko na wadanda suka mutu da kuma wadanda suke bin kudin kwantiragin aikin da suka yi wa Jihar Sakkwato.
15. An bayar da makudan kudi naira biliyan 2.6 ga babban sakatare, bangaren kula da harkokin Fansho da nufin cewa dukkan tsofaffin shugabannin Jihar Sakkwato da suka hada da Marigayi Dokta Garba Nadama, Malam Yahaya Abdulkarim, mataimakimsa marigayi Ahmed Muhammad Gusau, Dokta Attahiru Dalhatu Bafarawa, Chiso Abdullahi Datyijo, Dokta Aliyi Magatakarda Wamakko, Muktar Shehu Shagari, Abdullahi Balarabe Salame da Lawal Zayyana, an biya su kudin da ya dace a biya su kamar yadda dokar kasa tace tare da sauran ma’aikatan da suka ajiye aiki daga shekarar 2007 zuwa 2015 da a lokacin mulkin Wamakko da ya yi na shekaru Takwas yaki biyansu. Sai kuma wadansu makudan kudi naira miliyan dari biyu (200) da kuma wadansu miliyan 100 an fitar da su ga kwamitin domin a biya kudin jami’an Gwamnatin da suka yi ritaya daga shekarar 2015 zuwa 2016.
16. Za a iya ganin cewa Gwamna Aminu ya yi amfani da kudin da ya samu daga Gwamnatin tarayya ya biya kudin wadanda aka zaba a tsarin Dimokuradiyya tun daga shekarar 1984 zuwa 2007 ya kuma biya kudin ariyas daga shekarar 2007 zuwa 2015 wadanda Wamakko ya ki biyan ma’aikatan da suka ajiye aiki. Na ce ya ki yi ne saboda a duk tarihin Jihar Sakkwato, banda Ahmed Aliyu, ba wanda ya samu irin makudan kudin da ya samu daga asusun Gwamnatin tarayya kamar Gwamnatin Wamakko. Kuma gwamna Aminu ya biya kudin ma’aikatan da suka ajiye aiki na shekaru biyar sai kudin ajiye aiki na ma’aikatan da suka ajiye aiki daga kananan hukumomi.
17. Idan da Wamakko ya biya mutanen dasuka yi ritaya a lokacin Mulkinsa kamar yadda tsohon Gwamna Bafarawa ya yi da ba za a samu wani tsohon bashin kudin wadanda suka ajiye aiki ko ritaya ba, da har Gwamna Aminu zai bari wanda kuma shi Gwamna Ahmed ya gada.
18. Yanzu dai Za’a dai a iya cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya Gaji bashin kudin wadanda suka ajiye aiki wanda Aliyu Magatakarda Wamakko ya bari a lokacin Gwamnatinsa, amma ba Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ba.
19. Saboda haka, Gwamna Ahmed Aliyu ya dace ya duba yuwuwar ware naira biliyan biyar ya fara biyan kudin wadanda suka ajiye aiki ya kuma biyo bayan wannan da kudi naira miliyan dari biyar (500) a kowane wata, idan yayi haka a lokacin da zai cika shekaru biyu a shekara mai zuwa zai iya biyan dukkan mutane dari hudu da suka ajiye aiki, wadanda ya gada a sanadin bashin da ubangidansa Aliyu Wamakko ya barwa gwanna AminunWaziri Tambuwal.
Wannan fa zai iya yuwu wa sai dai idan ya na son gaya mana cewa dukkan kudin da Gwamnatin ta samu tuni an kashe su baki daya a wajen sayen motoci, da kuma zagaye wasu wurare da waya, samar da fitilun kan hanya da kuma abin da aka kammala kwanan nan wanda aikin Gwamnatin tarayya ne na gyara sansannin alhazai na filin Jirgin sama kuma tuni Iska da aka yi kwanan baya ta lalata shi bayan an yi bikin bude shi da kwana daya. A bangaren aikin gyaran tituna da ake yi a cikin garin Sokoto, shin za mu iya danganta shi da irin aikin tituna da ake yi a Jihar Zamfara, duba da inganci da kuma kwakwaro? Amsa dai ita ce A’a.
20. A karshe kamiin kammala wannan rubutu, zan bayar da shawara ga Gwamna Ahmed Aliyu Sakkwato da ya daina Dorawa tsohon Gwamna Sanata Aminu Waziri Tambuwal laifi, kawai domin Gwamna Ahmed Aliyu ya kasa cika alkawulan da ya yi wa jama’ar Jihar Sakkwato musamman ma mazauna karkara da har a yanzu suke sauraren ganin an zo an Dora masu koda bulo kwara daya ne da sunan za a yi masu wani abu na ci gaban rayuwarsu a karkashin Gwannatin Ahmed Aliyu Sakkwato. Saboda haka ne ya dace da yayi duba na tsanaki ga kudirorin Gwannatinsa guda Tara ya duba sosai ya ga ko ya na samun wani ci gaba ko A’a.
21. A cikin wannan shekara daya da wannan gwannati ta Ahmed Aliyu tayi tana jagorancin jahr Sokoto, mafi rinjayen al’ummar Sakkwato nada ra’ayin cewa Gwamna Ahmed Aliyu Sakkwato ya fadi kasa warwas inda aka aza shi a ma’auni domin ya kasa cika alkawuran da ya yi wa jama’a.
22. Zan duba wasu sauran bangarori a rubutun gaba.
HUSSAINI NA-HANTSI GADABO, DAGA KARAMAR HUKUMAR GADA