Related Articles
Imrana Abdullahi
Samakon carudewar al’amura yasa a dole shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keta ya ajiye aikin shugabancin kasar.
Indai za a iya tunawa al’amura sun dade da shiga wani mawuyacin hali a kasar, wanda sakamakon haka wadansu yan adawa da Gwamnatin kasar suka ce sai lallai shugaban tare da mukarraban Gwamnatinsa sun sauka daga mulkin kasar.
Biyo bayan irin matsalar da ake ta rade radin an samu na cewa wai sojoji sun kama jiga jigan da suke jagoranci a kasar wanda idan hakan ta faru lamarin ya zama juyin mulki kenan.
Kamar yadda bayanai daga kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen Afrika suna bayyana cewa kungiyar ta fara yin Allah wadai da halin da aka shiga a kasar ta Mali.
Bayan haka kuma sun Dakatar da kasar daga jerin kasashen Afrika da suke iya daukar duk wani mataki na fada aji, kamar yadda wakilin kafar yada labarai ta Al Jazeera Ahmed Idris, da ya aika masu da labari daga Abuja babban birnin Nijeriya
A cikin wata sanarwa kuma su dai kasashen na tarayyar Afrika sun rufe kan iyakokinsu kuma za su sanya wa Mali takunkumi idan aka ci gaba da rikicin
Kamar yadda ya bayar da sanarwa da aka yada a kafar yada Labaran Al Jazeera Talbijin shugaban Kasar Mali din ya bayyana ajiye aikinsa na shugabancin kasar.
Kuma a halin yanzu daukacin kasashen duniya sun yi Allah wadai da halin da Kasar Mali ta shiga ciki inda suka ce ana kokarin tabbatar da haramtacciyar Gwamnati da ta sabawa tsari.