Home / Labarai / An Yi Zana’izar Wada Maida

An Yi Zana’izar Wada Maida

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna na Daya Daga cikin dimbin mutanen da suka halarci Jana’izar marigayi Alhaji Wada Maida
Fitaccen dan Arewa na farko da ya nunawa mutanen Arewa cikakke kishi da kauna musamman a lokacin da aka nada shi ya shugabanci kamfanin dillancin labaran Nijeriya, inda ya dauki jama’a da dama aiki a wurin wanda hakan yasa mutane suka san ma me ake nufi da kamfanin dillancin Labaran Nijeriya.
An dai yi sallar jana’izar tasa ne a masallacin Area one da ke Garki babban birnin tarayya Abuja.
An dai gudanar da Sallar Jana’izar ne da misalin karfe 1:30 na ranar yau Talata.
Gwamna Masari ya jajantawa iyalai da yan uwan Marigayi Alhaji wada Maida bisa rashin da aka yi wa kasa baki daya.
Marigayin dai ya taba zama mai magana da yawun tsohon shugaban mulkin soja shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari lokacin yana mulkin soja a wancan karon.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.