Home / News / Shugabancin APC Na Riko Bai Hana Ni Aiki – Mai Mala Buni

Shugabancin APC Na Riko Bai Hana Ni Aiki – Mai Mala Buni

Shugabancin APC Na Riko Bai Hana Ni Aiki – Mai Mala Buni

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa Alhaji Mai Mala Buni ya bayyana cewa shugabancin APC baya hana shi yi wa jama’ar Yobe aikin da suka zabe shi ya yi masu.
Gwamnan ya bayyana cewa zamansa na Gwamnan Jihar Yobe ya samu nasarari da yawan gaske domin inganta rayuwar jama’a Jihar Yobe a fannoni daban daban.
Da suka hada da bangaren Ilimi,lafiya, samar da Tituna, Noma da dai fannoni da dama.
“Mun kwashi mata da a yanzu suke horon zama Likitoci a Jihar da kuma mata da yawa da aka saka su a cikin Gwamnatin Jihar Yobe a mukamai da ke bangarori daban daban wanda a hakan yasa ana damawa da mata a cikin Gwamnatin Yobe”.
Gwamnan ya ce mata ne za su iya zama a garuruwan da suke in ba aure ne zai dauke su ya kai wani wuri ba don haka za su iya zama tare da jama’ar garuruwansu a koda yaushe.
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin bbc hausa da suke tabbatarwa tare da hadin Gwiwar gidauniyar Maccathor shirin da aka yi wa lakabi da A Fada a cika, inda ake tace Gwamnoni ta hanyar amsa tambayoyi daga jama’ar Jihar daban daban.
Gwamna ya ci gaba da cewa aikin shugabancin APC bai taba hana shi yi wa jama’a aiki kamar yadda suka zabe shi ya yi, kuma inda yana hanani yin aiki ai ba zan karbi aikin ba.
“Kuma ni na zama Gwamna ne ta hanyar jam’iyya don haka jam’iyya ce ta samar da ni, kuma mutanen Jihar Yobe suka zabe ni”.
Ya ce ” Babu ta yadda za a yi a wata bai yi kwanaki uku a Yobe ba, kai a sati ma ina yin kwanaki uku a Jihar Yobe, kuma zamani ne na hanyoyin sadarwa na zamani ko a yanzu za a iya aiko mini da sako da ake bukatar amincewa ta kuma zai iya yin aiki don haka ko Bana cikin Jihar Yobe aiki ba zai tsaya ba ko kadan”.
Gwamna ya bayyana matsalar ciwon Koda da ake samu a Jihar da cewa binciken kwararriya Maimuna Waziri ya bayyana masa cewa matsalar ruwa ne da suke amfani da shi kuma ana nan ana kokarin samun maganin matsalar.
“Muna kula da masu fama da wannan matsalar ta ciwon Koda kyauta wanda sanadiyyar hakan har wadansu ma da ba yan asalin Yobe ba sukanci gajiyar hakan”.
Gwamna Mai Mala Buni, ya kuma bugi gaban cewa a halin yanzu ba a bin Gwamnatinsa bashin Albashi ko na sisin Kwabo saboda duk 24 ga wata yana biyan albashi, wanda hakan na Sanya farin ciki ga dimbin jama’ar Jihar Yobe.
Ya shaidawa bbc hausa cewa ya samu nasarari sosai a fannin ilimi wanda sakamakon hakan an samu nasarar ci gaban ilimi a Jihar Yobe wanda sakamakon jarabawar da ya fita kwanan nan ya tabbatar da hakan sabanin yadda lamarin yake a can kwanakin baya.
“Ko a fannin Noma ma mun raba Tarakatocin Noma ga manyan Manoma da matasa da kuma yan kasuwa domin a bunkasa lamarin harkar Noma a Jihar Yobe

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.