Home / Big News / Shugabannin Rundunonin Tsaron Nijeriya Sun Je Jihar Borno A Karon Farko

Shugabannin Rundunonin Tsaron Nijeriya Sun Je Jihar Borno A Karon Farko

Shugabannin Rundunonin Tsaron Nijeriya Sun Je Jihar Borno A Karon Farko
Mustapha Imrana Abdullahi
Sababbin Shugabannin Rundunonin tsaron Nijeriya sun kaiwa Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zullum ziyarar farko tun lokacin da suka kama aiki
A lokacin ziyarar Gwamnan ya bukace su da su ci gaba da samun kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da kasashen Chadi,Nijar da Kamaru, ya kuma fadakar da su a kan su rika sauraren masu kalubalantarsu.
Shugabannin Rundunonin tsaron da Buhari ya nada bayan da wadancan suka ajiye aiki duk sun yi alkawari  kara kwazon aiki a wajen fada domin kare kasarsu Nijeriya.
An dai nada su ne a sababbin mukamai daban daban domin su shugabanci rundunoni yakin sama da na ruwa sun kai ziyarar farko Jihar Borno, da ta kasance a matsayin cibiyar yaki da Boko Haram inda a lokacin ziyarar suka gana da Gwamna Babagana Umara Zulum a Maiduguri.
Tawagar dai ta kunshi Mejo Janar Leo Irabor, sai Mejo janar Ibrahim Attahiru, said kuma shugaban sojan sama Awwal Zubairu Gambo da kuma shugaban sojan Ruwa Isiaka Oladayo Amao, da suka kaiwa Gwamnan Jihar Borno ziyara a gidan Gwamnati a ranar Lahadi.
Shugabannin rundunonin tsaron dai an nada su ne a ranar Talatar da ta gabata wanda shugaba Muhamamdu Buhari ya yi.
Gwamna Zulum, lokacin da yake jawabi ga shugabannin rundunonin tsaron ya yi kira da a samu cikakken hadin kai da jami’an sojojin da suke a wadansu kasashe makwabta da suka hadar da Chadi,Camaru da Nijar.
 Zulum ya kuma bayyana cewa samun bayanan sirri ne ainihin mabudin ssmun nasara da yaki da yan Ta’adda don haka ya zama wajibi a samu hadin kai tsakanin jami’an soja da kuma al’ummar gari a ko’ina
Gwamnan ya kuma bayar da tabbaci ga shugabannin rundunonin tsaron cewa Gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya da nufin bayar da duk wani taimako ta yadda za a samu nasarar yakin da ake yi.
Zulum ya kuma shawarci sababbin shugabannin rundunonin tsaron su rika karbar suka da aka yi da kyakkyawar manufa domin kara inganta aikinsu a koda yaushe.
” A tsari irin na Dimokuradiyya rundunar soja dole ne sai ta rika fahimtar suka daga mutanen kasar da take wa aiki. Don haka dole ne ku rika yin maraba da suka daga jama’ar kasa kuma ku rika daukarta da kyakkyawar manufa domin kara himmar yin aiki a dukkan inda kuka samu kanku”, inji Zulum.
Gwamnan Zulum ya bayyana cewa idan sojojin Nijeriya na son samun nasara SSI an samu ingantaccen hadin kai da yin aiki tare da Juna tsakanin dukkan jami’an tsaro, musamman tsakanin jami’an sojojin sama da na kasa.
Gwamnan ya kuma yi kira ga sojojin su tabbatar sun ci gaba da yin aiki domin hana yan Ta’adda shakar Iska ta hanyar rufe dukkan wata kafar hanya da za su yi Motsi daga wannan yanki zuwa wancan.
Jagoran tafiyar Mejo Janar Leo Irabor bayar da tabbaci ya yi cewa aikin jami’an sojan zai kara bunkasa domin kakkabe matsalar yan Ta’adda baki daya. Sai ya bukaci samun fahimta daga daukacin al’umma da su ci gaba da fahimtar a lokacin yaki da yan ta’adda.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.