Home / Labarai / Surukar Sanata Ahmad Makarfi Ta Rasu

Surukar Sanata Ahmad Makarfi Ta Rasu

 

 

….Muna Cikin Alhini Da Juyayi Kwarai

Daga Imrana Abdullahi

 

 

Allah ya yi wa Hajiya Fatima da aka fi Sani da Binta Magaji Muhammad surukar Sanata Ahmad Muhammad Makarfi rasuwa.

Marigayiya Fatima Magaji Muhammad ita ce mahaifiya ga matar Sanata Makarfi wato Hajiya Asma’u Ahmad Muhammad Makarfi.

Babban dan marigayi Alhaji Magaji Muhammad, Murtala Magaji Muhammad ya tabbatar da rasuwar mahaifiyarsu inda ya bayyana mutuwar da cewa wani abu ne da ya zo masu cikin gigita da kuma damuwa kwarai.

“Domin ita dai ba wata jinya ta yi ba da ta dade, rashin lafiya ne kawai na dan wani lokaci kuma an je asibiti har an yi mata karin ruwa ta samu sauki ana karanta a waya duk ta na ta magana da mutane”.

Murtala Magaji Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a wurin karbar gaisuwar ta’aziyyar marigayiyar da ake yi a yanzu haka a gidan Mahaifinsu da ke Unguqar Sarki Kaduna.

Murtala Magaji Muhammad ya ce marigayiya Fatima Binta Magaji Muhammad ta rasu ta bar yaya Goma daga ciki akwai Maza Biyar Mata Biyar.

“Akwai ni Murtala, Asiya, Zainab, Asma’u,Maryam, A’Isha sannan akwai Abdullahi akwai Gidado, Muhammadu Sani sai kuma akwai Muhammadu Sada sun cika yayanta Goma kenan.

Murtala ya ci gaba da cewa ta rasu ta na da shekaru 75 domin an haifeta a 1950 kuma tsakanin rasuwar marigayi Magaji Muhammad da ita mahaifiyarsu an samu shekaru Shidda da kwanaki Ashirin da Takwas.

“A kullum dan Adam ya na da tunanin cewa zai iya kai lokaci kaza ko shekaru Kaza, amma dai yadda Allah ya tsara ma kowa haka zai kasance. A takaice dai ba jinya ta yi ba sai dai ta yi korafin cewa ta na yin Zazzabi sai aka Kaita asibiti ta na kuma yin Amai sai aka duba ta aka yi mata karin ruwa da duk abin da ya kamata a ranar Laraba kenan ta na kuma yin hira da kowa har ma na yi sallama da ita, sai a ranar Alhamis misalain karfe biyu na Dare sai aka kira ni domin abubuwa sun canza cewa in zo asibiti lokacin da na zo har Allah ya dauki ranta don haka ba wai jinya ta yi ba lokaci ne dai kawai ya yi, kuma ko shi Mahaifin mu ma suk abin da ya faru kenan ba wata doguwar jinya ya yi ba.

Murtala Magaji Muhammad ya ce hakika sun yi juyin rashin Mahaifinsu da baki daya domin a dukkan rayuwarsu suna tare da su a koda yaushe, suna ta kokarin Dora mu a hanya ta kwarai don haka ba zamu ta na mantawa da su ba a rayuwa baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.