Home / News / Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Wata Kungiya Ta Yaba Wa Bola Tinubu

Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Wata Kungiya Ta Yaba Wa Bola Tinubu

Daga Imrana Abdullahi
Wata hadaddiyar kungiyar da ke fafutukar kare martaba da mutuncin yankin arewacin Najeriya baki daya ta yaba wa zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bisa yadda ya yi shuru ba tare da tsoma bakinsa na a kan batun shugabancin majalisar.
Kungiyar mai suna ( North west Progressive Forum) ta bayyana hakan ne ta bakin mai gayya mai aiki Nasiru Dan batta a wajen wani gangamin taron yayan kungiyar da aka shirya a wajen gana wa da manema labarai a Kaduna.
Kungiyar ta ce hakika wannan bawan Allah Bola Ahmad Tinubu ya cancanci a yaba masa kwarai saboda duk da irin matsin lambar da ke tattare da batun neman shugabancin kujerar majalisar da kusan kowane bangare na kasar nan ne kokarin sai an bashi ya Dare kujerar, amma zababben shugaban kasar bai yi wata magana ba.
A wajen taron manema labaran wanda ya yi gayya kuma ya karantawa manema labarai jawabin abin da ya tara jama’a Maza da Mata a wurin ya ce duk da wasu san yi wani zama daga bangarorin kasar nan musamman ma guda biyu a kan wane wuri ne ya dace su fitar da shugaban majalisar Dattawan Najeriya
“Hakan ya Sanya wannan kungiya mai albarka ta yi duba sosai da idanun basira kuma ta gano cewa bisa irin la’akari da yadda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Abubakar Yari Shatiman Zamfara ya bayar da cikakkiyar gudunmawa sa hadin kai tare da yin aiki tukuru har zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Tinubu samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a Jihar Zamfara da gagarumin rinjaye hakika Jihar ta cancanci a saka mata da abin alkairi kamar wannan kujera ta shugaban majalisar dattawa”.
“Duk wani yunkurin da wadansu mutane za su yi game da wannan batu na shugabancin majalisar Dattawa mu ba za mu da mu ba domin daman can kamar wata al’ada ce da ke cikin Dimokuradiyya”.
Wannan gagarumin taro ya tabbatar da cewa yankin Arewa maso Yamma ne ya bayar da yawan kuri’un da suka kai kashi 30 cikin dari na yawan kuri’un da suka kai Bola Ahmad Tinubu a kan karagar mulkin Najeriya da yake jiran shan rantsuwa a yan makonni masu zuwa, don haka muke ganin ya dace ace yaba kyauta tukwuici, wato a sakawa yankin arewa maso Yamma da kujerar shugabancin majalisar Dattawa.
“Hakan ya sa duk duniya baki daya ta tabbatar da cewa yankin Arewa ya taka rawa wajen zaben Asiwaju Bola Tinubu karkashin jam’iyyar APC”.
Kuma ya na da matukar muhimmanci kwarai a san cewa Bola Tinubu ya samu yawan kuri’u miliyan 8.79 a cikin yawan kuri’un da masu zaben shugaban kasa suka kada don haka daga ciki yankin Arewa maso Yamma ya bayar da yawan kuri’u kashi 30 ne a cikin dari na yawan kuri’un sai yankin Kudu maso Yamma kashi 25.9, yankin Arewa ta tsakiya kashi 20 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada a zaben da ya gabata  sai Arewa maso Gabas kashi 13.5 a cikin dari, yankin Kudu maso Kudu kashi 9.10 da kuma yankin Kudu maso Gabas kashi 1.45 a cikin dari don haka duba da irin kokarin da yankin Arewa maso Yamma ya yi hakika ya dace a saka masa da kujerar da tsohon Gwamna kuma tsohon shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya Shatiman Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Abikar ke nema na ya zama shugaban majalisar Dattawa ta Goma (10).
“Kuma sai muke ganin ya zama wani al’amari daban ace yankin da ya bayar da kuri’ar da ta zama kashi 1.45 a cikin dari na yawan kuri’un da aka kada wai suma har suna ganin sai a ba su shugabancin majalisar Dattawa ta Goma.
Danbatta ya kuma yi bayanin abin da taron yayan kungiyar ya cimma da suka hada da irin Dattawan da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nuna na yin Gum da bakinsa ba tare da ya Sanya baki a wajen batun shugabancin majalisar ba, hakika hakan ya zama kamar zinare ne.
“Muna yin kira ga masu kokarin yin amfani da addini daga yankin Kudu da su sake tunani a kan irin matsayin da suka dauka su kuma dauki hali irin yadda duniya ke ciki na tsarin tabbatar da gaskiya da adalci, wanda idan an bi hakan zai ba yankin Arewa maso Yamma wato dai Arewa maso Yamma hakki da yancin su nemi kujerar shugaban majalisar Dattawa.
“Muna yin kira ga zababben shugaban kasa, Jam’iyyar APC da dukkan masu ruwa da tsaki a duk inda suke a fadin tarayyar Najeriya da su hanzarta nuna cikakken hadin kai da goyon bayansu ga yankin Arewa maso Yamma kasancewarsa yankin da ya fi kowa ne yanki cancantar ya samu kujerar shugaban majalisar Dattawa da ta kasance kujera ta uku a Najeriya, kuma ofishin da ya kasance na biyu a kasa bayan ofishin shugaban kasa”, inji Dambatta.
Takardar da aka karantawa manema labaran dai na dauke da sa hannun Nasiru Dambatta, wanda ya shirya taron sai Moses Rkpeyong, shugaban yankin Kudu maso Kudu na kungiyar da ke fafutukar tabbatar da adalci da kuma samun dai- daito; Ifeanyi James jagoran samun sabon tsarin tabbatar da Dimokuradiyya a majalisa da Fatima Mohammed daga kungiyar samun dai daito tsakanin jinsi.

About andiya

Check Also

MAY DAY 2024: GOV. DAUDA LAWAL RENEWS COMMITMENT TO IMPROVE WELFARE OF ZAMFARA WORKERS

By; Imrana Abdullahi Governor Dauda Lawal reiterated his administration’s commitment to improving the well-being of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.