Home / Big News / Tarayyar Turai Ta Ɗauki Nauyin Shirin Zaman Lafiya Na Kuɗi Yuro Miliyan 5.1 A Zamfara

Tarayyar Turai Ta Ɗauki Nauyin Shirin Zaman Lafiya Na Kuɗi Yuro Miliyan 5.1 A Zamfara

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wani sabon gagarumin shirin Tarayyar Turai da darajar sa ta kai ma tsabar kuɗi Yuro Miliyan 5.1, wanda aka tsara domin ƙarfafa zaman lafiya, kwanciyar hankali da juriyar al’umma a yankunan da rikice-rikice suka fi shafa a Zamfara da Katsina.

An ƙaddamar da shirin mai suna ‘Conflict Prevention, Crisis Response and Resilience’ (CPCRR) ne a ranar Litinin a ɗakin taro na Rescue Hall da ke Gidan Gwamnati a Gusau, inda Tarayyar Turai ta bayyana cikakken goyon bayanta ga ƙoƙarin gwamnatin Zamfara na dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Gautier Mignot, Jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya, ya halarci taron ƙaddamar da shirin wanda zai gudana tsawon watanni 18.

Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar jakadan ta haɗa da shugabar Hukumar Ƙaura ta Duniya, wato ‘International Organization for Migration’, Dimanche Sharon, da shugaban IOM na yankin Arewa maso Yamma, Jean Nahesi Katumbakana.

Shirin na CPCRR, wanda EU ke ɗaukar nauyin sa tare da aiwatarwa ta hannun IOM tare da haɗin gwiwar Mercy Corps da Cibiyar Raya Dimokuraɗiyya (CDD), an tsara shi ne domin tallafa wa sama da mutane 95,000 kai tsaye.

Waɗanda za su amfana sun haɗa da ‘yan gudun hijira na cikin gida, masu komawa muhallansu, al’ummomin da ke karɓar baƙi, mata da matasa a ƙananan hukumomi goma, takwas a Katsina da biyu a Zamfara.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa muhimmancin shirin bai tsaya a kan takardu ko jadawalin ayyuka kawai ba, sai dai yana shafar rayuwar yau da kullum ta jama’a.

Ya ce, shirin yana nuna aniyar haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa wajen gina al’umma mai ƙarfi, haɗin kai da zaman lafiya.

Gwamnan ya jaddada cewa tun farkon wannan gwamnati, an ɗauki batun tsaro da muhimmanci ta fuskar fahimtar tushen matsalolin da ke haifar da rikice-rikice, ciki har da talauci, raunin cibiyoyi da rushewar amincewar jama’a da juna.

A cewarsa, waɗannan su ne ginshiƙan da ake la’akari da su wajen tsara manufofi da haɗin gwiwa da abokan ci gaba.

Ya ƙara da cewa, shirin na CPCRR zai cike gibin ƙoƙarin gwamnatin Zamfara wajen farfaɗo da tattalin arzikin matasa da mata, inganta haɗin kai tsakanin ma’aikatu da hukumomi, da kuma tallafa wa hanyoyin tattaunawar sulhu a matakin al’umma, bisa fahimtar cewa tsaro, ci gaba da kyakkyawan shugabanci suna tafiya tare.

A nasa jawabin, Jakadan Tarayyar Turai, Gautier Mignot, ya yaba wa Gwamna Lawal kan jajircewarsa da goyon bayan da yake bai wa abokan ci gaba, yana mai bayyana kwarin gwiwar EU cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da Zamfara mai kwanciyar hankali da makoma mai kyau.

A ƙarshe, Gwamna Lawal ya gode wa Tarayyar Turai da IOM tare da CDD da Mercy Corps, yana mai cewa gina zaman lafiya aiki ne na bai ɗaya da ke buƙatar haɗin kan kowane ɓangare na al’umma. Daga nan ya sanar da fara aiwatar da shirin CPCRR a hukumance a Zamfara.

About andiya

Check Also

AN Yaba Wa Manema Labarai A Najeriya

  Daga Imrana Abdullahi Fitaccen Dan takarar jurerar majalisar dattawa daga mazabar Kaduna ta tsakiya …

Leave a Reply

Your email address will not be published.