Daga Imrana Abdullahi
Daukacin jiga- jigai madu ruwa da tsaki da ke fada a ji a tarayyar Najeriya da yankin arewa maso Yamma da suka kasance yayan jam’iyyar APC sun zartar da hukuncin daukar matakin bai daya na goyon bayan shugaba Bola Ahmad Tinubu da kuma dukkan Gwamnonin yankin da suka kasance a karkashin APC mai mulki a kasar.
Sun dai dauki wannan matakin ne a wajen gagarumin taron jam’iyyar APC na yankin arewa maso Yamma kato na biyu da ya gudana a Kaduna karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa tsohon Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje.
A lokacin da suke kokarin tabbatar da goyon baya da hadin kai tsakanin yayan jam’iyyar domin bayyana manufarsu Gwamnan jihar Kaduna ne Sanata Uba Sani ya fara bayanin cewa ya na gayyatar shugaban majaliaar wakilai na kasa Dokta Abbas Tajuddeen da ya gabatar da wannan aniya ta su gaban jama’ar taron, haka kuwa aka yi nan take ya gabatar sai Gwamnan Jihar Kebbi ya goyi bayan kudirin nan take sai aka yi irin abin nan na majalisa domin jin ra’ayin marasa rinjaye da na madu rinjaye nan take masu rinjaye suka samu nasara don haka yankin na goyon baya dari bisa dari na tazarcen Tinubu a shekarar 2027 mai zuwa da nufin idan an zabe shi ya ci gaba da yin mulkin Najeriya.
Taron dai ya samu halaryar Gwamnonin Jihohin Kebbi, Kaduna, Jigawa da kuma mataimakin gwamnan Katsina Abdullahi Jobe.
Sai kuma ministoci da kuma shigaban majalisar wakilai da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da kuma masu riko da mukamai hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi
A waje daya kuma akwai tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Kwamared Sanata Shehu Sani, Sanata Abu Ibrahim da dimbin jiga jigan APC na Shiyyar.
Da yake gabatar da jawabi a wajen taron shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana irin kokari da aiki tukurun da shugaba Tinubu ke yi wajen ciyar da al’amuran tattalin arziki da sauran al’amura gaba ta yadda Najeriya za ta tserewa tsara a fadin duniya.
Ya kuma ce kamar yadda wadansu gwamnoni suka koma jam’iyyar APC da wasu yan majalisu daga yankin kudancin Najeriya, haka suke saran nan gaba kadan Gwamnonin Kano da Zamfara su koma APC daga yankin Kudu maso Yamma.
Shima a nasa jawabin shugaban majalisar wakilai ta kasa Dokta Abbas Tajuddeen, cewa ya yi karo na farko ba zao ba shugaban kasa damar sanin yadda al’amura suke ba don haka ya na da kyau a kara ba shi wata damar a kato na biyu domin ci gaba da aiwatar da ayyukan alkairin da ake yi a halin yanzu.
A wajrn taron an kuma jawo hankalin yauan jam’iyyar da su koma mazabunsu kowa ya kara bayar da himmar wajen fadakar da jama’a abin da gwambatin tinubu ke aiwatarwa a kasa baki daya.
Jihohi Bakwai ne suka hadu suka yi yankin arewa maso Yamma da suka hada da Jihar Katsina, Kano, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Jigawa da Jihar Kaduna da ta zama mai masaukin baki a waken taron na APC shiyyar arewa maso Yamma.