Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar matasan arewacin Nijeriya da ke fafutukar samar da zaman lafiya da kuma hadin kan siyasa (NOYPO) sun bayyana cikakken hadin kai da goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle game da irin matakan da ya dauka a kan harkokin tsaro a Jihar.
Sakataren kungiyar na kasa, Barista Abdullahi Aed Kalgo a cikin wani sako mai taken, “Yan bindiga: kalubalen tsaro a yankin mu, hakika Gwamna Bello Matawalle da gaske yake yi”, don haka kungiyar na yin kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamna Matawalle domin ciyar da kasa gaba.
Yan kungiyar sun bayyana cewa Gwamnonin jihohon da ke zagaye da Jihar Zamfara da suka hada da Sakkwato,Kebbi,Neja, Katsina da Kaduna na yin kira gare su da su hanzarta bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamna Matawalle domin samun damar aiwatar da ayyukan da ya Sanya a gaba wajen yaki da yan Ta’adda da ayyukansu baki daya da ya addabi yankin.
Yan kungiyar ta matasa sun bayyana cewa samun hadin kai tsakanin Juna zai taimaka kwarai wajen samun ingantattun bayanai daga Juna zai taimaka a samu ci gaban da ake bukata.
Kamar yadda kungiyar ta ce, “duba da irin yadda Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle yake aiwatarwa da sauran wasu mutane masu ruwa da tsaki, matakan za su taimaka kwarai a samu ciyar da kasa gaba musamman ta fuskar tsaro.
Ana sa ran Gwamnonin Jihohin Kebbi,Neja,Sakkwato da Katsina dukkansu za su yi koyi da irin wannan kokari na ta hanyar bayar da goyon baya da nufin a samu kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar yankin.
“Gwamnatin Jijar Zamfara ya dace ta dauki matakan yin horo mai tsanani ga duk wani gidan mai ko wasu jama’ar da suka ki bin wadannan matakai da Gwamnatin Zamfara ke dauka.
“Muna yin kira ga jami’an tsaro da su yi taka tsantsan wajen aiwatar da aikinsu musamman tabbatar da jama’a sun yi aiki da dokar.
“Matasan yankin arewacin Najeriya na goyon bayan Gwamnan Bello Muhammad Matawalle game da wannan matakin samar da tsaron da ya dauka da ake saran za su haifar da zaman lafiya a Jihar baki daya.
“Muna yin kira ga mutanen Zamfara su bayar da hadin kai da goyon baya ga Gwamnan Jihar Zamfara a game da wadannan matakan da ake dauka musamman wajen rufe kasuwanni da kuma takaita zirga zirgar jama’a da kayayyaki, ya dace jama’a su Sani cewa nan gaba kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamna Matawalle bisa matakan da yake dauka wajen yaki da matsalar tsaro, da ayyukan yan bindiga a Jihar”, kamar yadda yayan kungiyar ya bukata.