Shahararren gidan Talabijin din nan na Qausain TV, ya baiwa tsohon Manajan Daraktan Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Kasa, Alhaji Munir Ja’afaru lambar yabo ta “Award of Excellence”.
Shugaban Gidan Talabijin na kasa Malam Nasir Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ce wanda ya lashe kyautar, Ja’afaru, a halin yanzu yana rike da martabar masarautar Madakin Zazzau.
Idris ya lissafo kwararan dalilai da suka sanya gidan talabijin na Qausain ya yanke shawarar karrama Madakin Zazzau, inda ya nuna irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa ga al’umma da kasa baki daya.
“Alhaji Munir Ja’afaru ya yi fice a matsayin lauya, kwararren ma’aikacin aikin Gwamnati, shugaba da kuma babban dattijo mai kishin kasa. Jagorancinsa nagari a bangarori daban-daban ya cancanci a yaba wa Najeriya da al’ummarta,” inji Idris.
Da yake karbar lambar yabo, dattijon ya nuna jin dadinsa ga gidan talabijin din da suka same shi da ya cancanci karramawar, inda ya ce ya yi matukar farin ciki da karramawar da bai yi tsammani ba.
Ya kuma yaba wa cibiyar sadarwar saboda abubuwan da ke cikin shirye-shiryenta na musamman da kuma ayyuka masu mahimmanci, waɗanda suka yi tasiri ga al’ummar Najeriya da ma fiye da haka.
“Ba na tsammanin irin wannan karramawa daga kowace kafa. Na yi matukar mamakin hakan kuma na gode maka da ka same ni na cancanci wannan karramawa”.
“Ni da iyalina muna sauraron gidan talabijin ku a koyaushe, muna jin daɗin shirye-shiryen fadakarwa da ilimantarwa cikin harsunan Hausa da Ingilishi da Larabci,” in ji shi.
Yayin da yake taya shugaban Qausain na kasa murnar jajircewar sa, Ja’afaru ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu domin amfanin Nijeriya da ‘yan Nijeriya.
A shekarar 2021, an daukaka Munir Ja’afaru daga Yariman Zazzau zuwa mukamin Madakin Zazzau, wanda shi ne babban mukamin basarake a Masarautar Zazzau, wanda mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli ya bashi.