Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu na cewa tsohon shugaban kasar tarayyar Cif Ernest Shonekan da ya shugabanci Gwamnatin rikon kwarya da ya Gaji mulkin wajen shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai murabus, ya rasu ya na da shekaru 85.
Shenekan ya rasu a wani asibiti a Lekki da ke cikin Legas, a shekaru 85.
Ya dai shugabanci Gwamnatin rikon kwarya ne daga watan Agusta 26 da Nuwamba 17, 1993, wanda daga baya ya fita daga cikin mulki sakamakon juyin mulkin da marigayi tsohon shugaban kasa ya Sani Abacha ya jagoranta.