Home / Labarai / Uwar Gidan Shugaban Kasa Ta Bayar Da Tallafin Karatu Miliyan 1 Ga Daliban Jami’ar FUDMA

Uwar Gidan Shugaban Kasa Ta Bayar Da Tallafin Karatu Miliyan 1 Ga Daliban Jami’ar FUDMA

 

Daga Imrana Abdullahi

 

Uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin karatu na miliyan daya ga daliban jami’ar Gwamnatin tarayya ta Dutsinma, da ke Jihar Katsina, wadanda yan bindiga masu satar mutane suka sace kwanan baya, a ranar 4 ga watan Okutoba.

 

 

Uwargidan shugaban kasar wadda take tare da Mai dakin mataimakin shugaban kasa Nana Shettima, a ranar Asabar a Abuja, sun mika wa kowane daya daga cikin daliban da aka kama naira miliyan daya da kuma na’ura mai kwakwalwa ( Kwamfuta), wadanda aka sace lokacin suna a wurin gidan da suke zaune a ranar 4 ga watan Okutoba.

 

 

 

She said the scholarship would run for four years, being the period the girls, Safiya Mutu, Hasiya Abubakar, Ramat Adam, Fatima Abdullahi and Fatima Mohammed, would spend in school.

 

Dukkansu daliban sun kasance suna matakin karatu aji na daya ne wato (100- level) ta ce Gwamnatin tarayya na ganin muhimmancin karatun da suke yi da kuma tsaron lafiyarsu, sabida haka ne ta yi alkawarin bayar da naira miliyan 2 da kuma mataimakin shugaban jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma Farfesa Armaya’u Bichi, Maura miliyan 1.

 

 

” Tun lokacin da aka dauke ku a ranar 4 ga watan Okutoba, muna cikin yanayi mai tsanani kuma na jin zafi sosai, tun daga kan iyayen ku, Malamanku da dai sauran yan Najeriya”

 

Kuma tun a wancan lokacin muka mika komai ga Allah da kuma jami’an tsaron mu muke ta yi masu addu’ar samun nasara Allah yasa mu dawo lafiya

 

 

Bayan samun akalla kwanaki 70 a hannun masu satar mutane suna yin Garkuwa da su, sai ga shi a yau muna samun wata damar yin farin ciki da annashuwar dawowarku cikin al’ummar kasa”.

 

“Za kuma mu ci gaba da duba ku sosai tun daga makaranta har zuwa samun ci gaban lafiyarku”.

 

 

 

 

 

 

 

Samun ilimi mai inganci ne ainihin Makamin yaki da ta’addanci don haka yana da matukar muhimmanci ku ci gaba da neman ilimi, saboda haka sai ku tuna yadda rayuwarku take a can baya da kuma na al’ummar da kuke ciki da nufin yaki da ta’addanci da kuma sauran miyagun dabi’u baki daya

 

Ta kuma yabawa dukkan jami’an tsaro baki daya bisa ayyukan da suke yi na ganin an samu nasarar da ya dace.

 

 

 

 

 

 

Kuma muna fatan wannan jarabawar da kuka samu za ta kara maku kwarin Gwiwar tashi tsaye wajen ayyukan ku da kuma karatun ku ta yadda kasa za ta yi alfahari da ku baki daya”.

 

 

 

 

Da yake gabatar da jawabi wani babban jami’i a ofishin mai bayar da shawara a kan harkokin tsaro na shugaban kasa Birgediya Janar. Olutayo Adesuyi, cewa ya yi wannan taron haduqar da uwargidan shugaban kasa ta yi abu ne mai matukar amfani kasancewar lamarin ya nuna irin kokari da tausayin Gwamnatin tarayya tare da taimakawa wadanda aka sace din.

 

 

Da suke mayar da jawabi kowace daliba godiya ta yi ga uwargidan shugaban kasa Sanata Tinubu bisa irin taimakon da ta yi masu.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.