Daga Imrana Abdullahi
An yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su kara himmatuwa wajen hadin kai da taimakon kansu da kansu
Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun ne ya yi wannan kiran jim kadan bayan kammala rufe wa’azin watan Ramadana na Bana da ya gudana a Masallacin tunawa da marigayi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi da ke a Rigachikun Kaduna tarayyar Najeriya.
Shaikh Yusuf Sambo ya ce shi babban sakon da yake da shi ga daukacin al’ummar Musulmi shi ne kowa ya yi hakuri a hada kai domin kalubalen da ke gaban Musulmin Najeriya da Kalubalen da ke gaban Musulmi a duniya, hakika duk wadansu rarrabuwar Kawuna da rabe- rabe lallai ba namu ba ne.

“Idan mun zo muna fadan cikin gida wannan duk yamu- yamu ne, amma idan duniya da Yahudawa da wasu da ba mu ba, ayi hakuri kowa ya boye rowar ransa ayi hakuri a hada kai a tunkari kalubalen da ke gaban mu, sai kuma abu na biyu akwai wadansu a cikin mu suna yada cewa wai su ba za su jefa kuri’a ba wai don murde rabe ake yi lallai hakika wannan shi ne kuskure babba mu kasa fitowa mu jefa kuri’a. Ai akwai kuri’ar da idan an jefa ta ta fi karfin a murde saboda haka ina kira ga al’ummar Musulmi da mu fito mu jefa kuri’a mu fito mu yi zabe shi ne zaman lafiyar mu in mun yi sai mu mayar da al’amarin mu ga Allah shi ne mai hukunci”.
A game da ziyarar da kungiyar jama’atu ta jihar Kaduna ta kawo masu a wajen rufe tafsirin kuwa, wallahi naji dadi kwarai kwarai da gaske domin ita jama’atunnasarul Islam ita ce Kungiyar farko da ta jagoranci duk irin wadannan ayyukan saboda haka kamar yadda na ambata don haka ya dace ta motsa ta yunkura a ci gaba da aiki tare ta yadda abubuwan mu za su yi kyau.
Sambo Rigachikun ya kuma ce da ikon Allah za su ci gaba da bayar da gudunmawar shawarwari a kan abin da ya dace mu yi da ikon Allah.

Sai kuma ya yi karin haske a game da irin yadda wadansu yan majalisar da ake da su daga arewacin Najeriya suke yin watsi da batutuwa da suka shafi yankin idan aka duba irin aikin hanyar Legas zuwa Kalaba, ana kashe makudan kudade masu yawa, amma mu ku duba a nan hanyar Kaduna zuwa garin Jos babu kyau, Kaduna Kano, Kaduna Abuja duk ba kyau ga dai hanyoyi nan sun lalace kuma duk hanyoyin mu idan za a yi su ba su kai tsadar waccan da ake yi ba kuma amma sai su ba za su yi magana ba a matsayinsu na yan majalisa, hakika wannan kuskure ne.
THESHIELD Garkuwa