Home / Labarai / Yaki Da Cin Hanci Ya Fi Karfin Gwamnati – Dokta A J Suleiman

Yaki Da Cin Hanci Ya Fi Karfin Gwamnati – Dokta A J Suleiman

Yaki Da Cin Hanci Ya Fi Karfin Gwamnati – Dokta A J Suleiman

Imrana Abdullahi
Wani Malamin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Dokta Ahmad Jibril Suleiman ya bayyana cewa yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nijeriya ya fi karfin Gwamnati ita kadai don haka dole sai kowa ya bayar da cikakkiyar gudunmawarsa domin a yaki wannan mugun abu.
Dokta A J Suleiman wanda Lauya ne kuma Malamin lauyoyi da ya karantar da lauyoyi da dama a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya bayyana cewa yana fafutukar fadakarwa a kan zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasa.
“Ina da kungiyar Ambassadors Of Peace and Social Welfare domin a samu nasarar da kowa ke bukata”.
Dokta A J Suleiman ya bayyana cewa babu ta yadda za a yi mutanen kasa su rika zaton cewa yaki da irin wannan mummunan abu ayi zaton Gwamnati ce kawai za ta yi yaki da shi.
“Sai kowa ya bayar da hadin kansa da goyon baya sannan za a samu nasara saboda kusan ya shafi komai na rayuwar jama’a baki daya, yana lalata tattalin arzikin kasa, halayyar jama’a da dukkan fannonin rayuwa duk wannan matsalar ta shafi ko ina don haka sai kowa ya tashi tsaye”.
Kuma wani al’amari ne da sai kowa ya tashi tsaye a kansa Malaman addinin Islama da na Kirista domin a kaucewa samun mummunar asara da za ta iya kai mu ga zubar da jini domin mugun lamari ne da ya kai ga  haifar da ci baya iri iri wanda ya dade yana damun Nijeriya tsawon lokaci.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.