Home / Labarai / Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Yan Kara Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Yan Kara Jihar Katsina

Kamar yadda muka samu sahihan rahotanni daga mazauna garin Yan Kara da ke cikin karamar hukumar Faskari bayanan sun tabbatar da cewa Ayyukan yan bindiga na kara ta’azzara a Jihar Katsina.
Kamar yadda wasu mutanen da suke cikin garin Yan Kara suka shaidawa wakilinmu cewa yan bindigar sun samu shiga garin ne da Yammacin yau Juma’a da misalin karfe shida saura yan mintuna.
Kamar yadda wani mazaunin garin ya tabbatar mana cewa wani bawan Allah da yazo domin yin sayayyar irin shuka a shago su cikin garin yan kara, sai suka ji kawai mutum na amsa waya yana ta salati, da suka tambaye shi meke faruwa sai ya ce ai yan ta adda ne a cikin garin su, sai ta fi sai suka ce masa ina zaka ka zauna nan kawai tun da garin ku baya shuguwa.
Ashe a lokacin da suke maganar ma har sun Baro wannan kauyen suna cikin garin Yan Kara, ashe dalilin zuwansu kauyen shi ne sun je satar shanu ne tun da suka ga ba shanun suna cikin garin yan kara inda mai su ke kawo su domin su kwana da safe ya tafi kiwo, shi ne suka biyo cikin garin Yan Kara din.
Kamar yadda mutanen garin ke tabbatarwa da wakilinmu cewa su yi wa jama’a rauni kuma sun ta fi da mutane biyu kai har ma da asarar rayuka duk a wannan garin na Yan Kara.
“Wallahi mamayar my suka yi domin ba wanda ya yi tsammanin za su shigo cikin garin mu a yanzu, amma tare da yan sa kai da jami’an tsaro an mayar da su baya sun koma inda suka fito can Yamma da Garin Yan Kara”.
Kamar yadda wakilinmu ya tattaro sahihan bayanai na cewa kusan kauyuka Goma sha hudu da suke Yamma da Faskari duk mutanen cikinsu sun fice daga garin sun zama yan gudun hijira ko dai sun samu matakan a cikin Yan Kara ko sun koma garin Funtuwa suna Labe a gidajen yan uwa da abokan arziki.
“Don haka muke kira ga shugaba Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari su tuna da alkawari da rantsuwar da suka yi na kare lafiya da duniyar jama’a tare da samar da ingantaccen tsaro”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.