Related Articles
Yan Kungiyar Kwadago Sun Janye Yajin Aiki A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Yayan kungiyar Kwadago ta kasa a tarayyar Nijeriya sun bayar da sanarwar janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da suke yi a Kaduna.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaba da mataimakinsa Kwamared Ayuba Wabba da kwamared Alhaji Najibu Ahmad Yasin da suka kasance a cikin garin Kaduna tun ranar Lahadin da ta gabata ana aiwatar da ayyukan kwatar yancin jama’a.
Kwamared Ayuba Wabba ya bayyana cewa kasancewar ya karbi takardar kira domin a zauna Teburin tattaunawa daga Ministan ma’aikatar Kwadago sun zauna da majalisar kolin kungiyoyin da ke karkashin kungiyar Kwadago ta kasa baki daya.
“Bisa hakan a yanzu mun cimma matsayar janye yajin aikin da ake cikin yi har sai an je Abuja an tattauna da ministan kwadago bisa kiran da ya yi wa bangaren uwar kungiyar kwadago ta kasa da kuma bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna domin tattaunawa game da matsalolin da suka haifar da yajin aikin”, inji yan kwadago.
Najib Ahmad Yasin, mataimakin shugaban kungiyar Kwadago ta kasa ya ce nan da ranar 25 ga wannan watan za a sake yin wani zama a Abuja domin tattaunawa ta musamman tsakanin yayan kungiyar kwadago ta kasa.