Home / Labarai / Yan Majalisar Ribas Sun Amince Da Tinubu Ya Zarce Karo Na Biyu

Yan Majalisar Ribas Sun Amince Da Tinubu Ya Zarce Karo Na Biyu

 

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta amince da irin ayyukan ci gaban da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yi wa Jihar domin dimbin Jama’a su amfana.

Majalisar sun bayyana amincewarsu ne a wajen wani taron da majalisar ta gudanar a yayin Zaman majalisar inda suka fayyace dukkan ayyukan alkairin da shugaba Tinubu ke aiwatar ga jama’ar Jihar.
Yan majalisar sun ce ban da ma irin yadda kowa ya shaida ayyuka a kasa da suka hada da rage Farashin Kayan Abinci kamar Farashin Shinkafa da kuma raguwar Farashin dalar Amurka Wanda kowa ya San hakan.
Abin jira a gani a nan Shi ne yadda Yan majalisar za su jajirce wajen nemawa shugaba Tinubu yarda da amincewar Jama’a domin samun kuri’ar da ta dace.

About andiya

Check Also

Zanga – Zanga Ba Abin Alkairi Bace- Bashir Nafaru

An bayyana batun Zanga Zangar da wadansu mutane ke kokarin shiryawa a Majeriya da cewa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.