Home / Uncategorized / Yan Majalisar Wakilai Na PDP Uku Sun Koma APC A Majalisa

Yan Majalisar Wakilai Na PDP Uku Sun Koma APC A Majalisa

Wadansu yan majalisar wakilai guda uku daga Jihar Katsina sun sauya sheka zuwa APC a majaliaar wakilai ta kasa.

Sakamakon hakan ne ya sanya Gwamnan Jihar Katsina da kansa ya kasance a majalisar wakilan domin shaida faruwar hakan a majaliaar wakilai ta kasa da ke Abuja.

Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Honarabul Balarabe Dubai mai wakiltar kananan hukumomin Bakori da Dana’s sai Honarabul Iliyasu Abubakar mai wakiltar kananan hukumomin Batsari da Safana da kuma Dan – Musa sai kuma na ukun Honarabil Salisu Yusuf Majigiri mai wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi duk suna a matsayin wakilai ne a majalisar.

Gwamna Dikko Radda tare suka isa majalisar wakilan tare da tsohon Gwannan Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema kuma ya samu tarba da maraba ne aka kuma shigar da shi cikin majalisar daga shugabannin majalisar.
Shugaban majaliaar ne Honarabul Abbas Tajuddeen ya sanar da batun komawar yan majalisar guda uku.

 

 

A cikin takardar sanarqar da suka mika duk yan majalisar sun sanar da cewa batun rabuwar Kawuna rarrabe rarrabe da kuma rigingimu a cikin PDP tun daga jiha zuwa matakin jam’iyyar na kasa ya sanya suka dauki wannan matakin na komawa APC.

Jim kadan bayan da ya karanta takatdar da suka aiko wa majalisar na ficewa PDP’ sjugaban majaliaar Abbas ya sanar da cewa Gwamnan Katsina na cikin majalisar’ wanda kuma daga nan sai ta tashi a majalisar inda ya rika gaisawa da yan majlisar da suka sauya sheka da kuma gaiaawa da sauran shugabannin majalisar ta wakilai.

Ranar Alhamis ta kasance wata rana ce da wani muhimmin labari ke ta yawo ya na karade duniya daga majaliaar wakilai inda aka samu wata gagrumar Iskar sauya sheka daga jam’iyyar PDP da jam’iyyar Lebo suna komawa jam’iyyar APC.

Kwanaki biyu kafin faruwar wanna lamarin wadansu yan majalisu daga Jihar Delta suka fice daga PDP zuwa APC sai kuma wadansu guda biyu daga jam’iyyar kwadago ta LP daga Jihar Enugu suka koma PDP.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Hands Over MCHC Tsakatsa

By Lawal Gwanda A befitting Maternal and Child Health Centre constructed by Senator AbdulAziz Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.