Home / Lafiya / Yawuri Ta Zamo Matattarar Macizai –  Dokta Sununu

Yawuri Ta Zamo Matattarar Macizai –  Dokta Sununu

Mustapha Imrana Abdullahi
Honarabul Dokta Yusuf Tanko Sununu, dan majalisa ne mai wakiltar kananan hukumomin Yawuri, Ngaski da Shangwam a majalisar wakilai ta tarayya da ke Abuja ya bayyana matsalar maciji a matsayin abin da ke addabar Yawuri.
Dan majalisar Dokta Yusuf Tanko Sununu ya dai bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa da kafar Talbijin ta Farin Wata.
Honarabul Sununu ya ce kasancewar Yawuri ya zamo wurin da ke fama da matsalar annobar cizon majizai ya sa da kansa ya tashi tsaye wajen samawa jama’a sauki ta fuskar managin cizon Maciji.
“Hakika maganin Cizon maciji ya kasance mai tsadar gaske saboda ya na wuce naira dubu casa’in, to ina jama’a da suke a kauyuka za su iya wannan kuma ga lamarin Allah dai ya saukar da macizai a wannan wuri, a mafi yawan lokuta sai mutum da ya samu kansa cikin matsalar cizon maciji ya sayar da wata mihimmiyar kadara tasa da yake amfani da ita yau da kullum domin taimakon rayuwarsa
Hakan ya sa na tashi tsaye wajen nemo sahihin maganin cizon maciji saga manyan wuraren sayar da magani na duniya wanda a yanzu akwai isassun wadataccen maganin cizon maciji a asibitin Yawuri domin taimakawa jama’a, kuma koda mutum zai ce asibitin Yawuri na daya daga cikin masu wadatar maganin cizon maciji bai yi kuskure ba.
Honarabul ya kuma ce kasancewarsa na Likita wakilin jama’a ya yi wa mutane da yawa aikin gyaran idanu da ba su gilashin ido da kuma Magunguna kyauta
” Na kuma yi wa mata akalla dari hudu da Hamsin (450) aikin batun haihuwa duk kyauta, da Gona Gidajen Likitoci da masu aikin asibiti a asibitoci daban daban domin su daina cewa sai sun koma garuruwansu sannan da safe su dawo, to, idan rashin lafiya ya kama mara lafiya da Daddare fa.
Ya kuma yi alkawarin yi wa sauran mazabu biyu da suka rage masa aikin samawa jama’a lafiya kamar yadda ya yi wa sauran mazabun da yake wakilta.
“Buri na shi ne in aiwatar da wani umarnin da mahaifina ke gaya Mani cewa duk lokacin da na samu dama in taimaki talakawa don haka nake aiwatar da abin da nake yi kuma ina jin dadin hakan”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.