Home / Kasuwanci / Za A Bude Babbar Kasuwar Kaduna Gobe Alhamis

Za A Bude Babbar Kasuwar Kaduna Gobe Alhamis

 Imrana Abdullahi
Kamar yadda zaku iya gani a cikin hoton da ke cikin labarin nan za a iya tabbatar da cewa tuni aka kammala shirye shiryen sake bude babbar kasuwar kaduna da ake kira Abubalar Gumi da ke tsakiyar birnin Kaduna.
Ita dai wannan kasuwa an rufe ta ne tsawon watanni hudu da suka gabata saboda daukar matakan kariya ga cutar Korona da ta addabi duniya baki daya.
Mqnajan Daraktan hukumar da ke kula da kasuwar, Hafiz Bayero ya bayyana gamsuwar iron taimakon da Gwamna El- Rufa’I ke bayar wa domin kawo wa jama’a saukin rayuwa a lokacin yaki da cutar Korona.
Musamman ta fuskar taimakawa yankasuwar da batun rufe kasuwar ya shafa matuka.
Tuni dai aka sanar da yan kasuwar cewa batun bude babbar kasuwar zai zama kamar Gwaji ne ta fuskar bude sauran Kasuwannin baki daya.
Bayanai dai sun bayyana cewa kwamitin yaki da cutar Korona karkashin jagorancin mataimakiyar Gwamnan Jihar ba za su yi kasa a Gwiwa ba wajen rufe kasuwar idan aka ki bin ka’idojin da aka shimfida wajen yaki da cutar.
An dai samar da wadansu kayayyakin da suka hada da abubuwan wanke hannu da rufe baki da fuska tare da Robobin wanke hannu da abin auna yanayin zafin jikin mutum duk a matsayin ka’idar da za a bi kafin shiga kasuwar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.