Home / News / Za A Samar Da Kungiyar Wasannin Kwallon Kafa Ta Kaduna United – Sa’idu Bidis

Za A Samar Da Kungiyar Wasannin Kwallon Kafa Ta Kaduna United – Sa’idu Bidis

….Da kuma katafariyar cibiyar wasanni ta zamani a Kaduna

Daga Imrana Abdullahi

Malam Sa’idu Idris Dibis, mataimaki na musamman ne ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin wasanni, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Sanata Uba Sani za ta samar da sahihiyar ingantacciyar kungiyar kwallon Kafa ta “Kaduna United” domin kara inganta tattalin arzikin Jihar.

Sa’idu Idris Dibis da ake yi wa lakabi da Koch, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala gasar karshe  ta wasan kwallon kafa da JKD Academy suka shirya a tsakanin makarantun Sakandaren da ke cikin garin Kaduna.

Dibis ya ce hakika wannan rana da aka buga wasan karshe na wannan Kofi yazo dai – dai da ranar da ake ta bikin murnar samun nasarar Gwamna Uba Sani a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kaduna kamar yadda Kotun kolin Najeriya ta tabbatar masa a jiya Juma’a, haka kuma yazo dai- dai da ranar da Mahaifin wadannan yara da suka Sanya wannan Kofi har aka buga wasan karshe a ranar ne dai- dai da ranar haihuwarsa wato Dattijo Ambasada Yusuf Mamman, da yake cika shekaru Saba’in, don haka muna yi wa Allah godiya a kan hakan bisa gamsuwa da farin cikin da nake ciki kwarai.

Da akwai ainihin aikace- aikacen da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Sanya a gaba da nufin Farfado da harkokin wasanni a Jihar Kaduna.

“A cikin watanni Bakwai ko Takwas an fara samun tagomashi a harkokin wasanni a Jihar Kaduna, akwai shirye shiryen da ake yi domin bunkasa harkokin wasanni a Jihar Kaduna. Za a yi gudu wato tseren Dawaki, wanda tuni har Gwamnan Jihar Kaduna ya bayar da damar a kaddamar da shi domin murnar cika shekaru uku na Mai martaba Sarkin Zazzau , wanda lamarin zai zamo kamar na farko ne a Jihar Kaduna kuma da ikon Allah a karshen watan biyu za a kaddamar da wasan har tsawon kwanaki uku, muna fatan yan jarida za su taimaka mana wajen samun nasarar hakan”.

Bidis ya kara da cewa ” Gwamnan Jihar Kaduna ya bayar da damar yin gudun tsere wato maraton, kamar yadda kowa ya Sani an taba yin sa a shekaru biyu amma an canza mashi salo da nufin dawo da martabar Kaduna har an Sanya wa gasar suna Maraton Kaduna 2024 da yardar  Allah  muna tunanin bayan watan Azumi za a yi wannan gasar a watan hudu na Afirilu. Bayan haka kuma akwai wata gagarumar nasarar da Gwamnan Jihar Kaduna ya samu, a lokacin Gwamnatin da ta gabata an dawo wa Jihar Kaduna da filin wasanni na Ahmadu Bello hannun Gwannatin Jiha amma a takarda, amma a yanzu an yi kwamiti har yanzu Ahmadu Bello ta dawo a hannun Gwamnatin  Jihar Kaduna karkashin kulawar ma’aikatar wasannin Jihar Kaduna, kuma Gwamna bai yi kasa a Gwiwa ba yasa ayi gaggawa fara gyare gyare na dukkan filin wasan a mayar da ita ta zamani kuma nan ba da jimawa ba zaku ga yadda filin wasa na Ahmadu Bello zai kasance”.

Kuma ina fadi da babbar murya cewa a cikin kasafin kudin Bana Malam Una Sani ya Sanya a kasafin za a gina wata gagarumar cibiyar wasanni mai kyau ta zamani da a Kaduna za ta zama ta zamani, kuma za a mayar da filin wasanni na Jihar Kaduna ne da ke kan titin Indefendence cikin garin Kaduna ne za a mayar wannan katafariyar ciniyar wasanni ta zamani, ” kamar yadda wadanda suka san kasar Ruwanda akwai filin wasannin Kigali Arena, haka Gwamnan Jihar Kaduna ke sha’awar ayi irin ta ko wadda ta fi ta kyau tuni ya riga ya Sanya a kasafin kudin wannan shekara, da haka ne za a iya tabbatar da cewa Malam Uba Sani na son Jihar Kaduna ta wuce yadda aka Santa a da can a harkar wasanni kuma ta zamo mai amfani.

Hakazalika muna yin kyakkyawan shiri a kan samun kungiyar kwallon Kafa ta Kaduna United, kuma ba ta Gwamnati zalla ba, ta yan Kasuwa da Gwamnati wanda ba za ta zamo a buga bane kawai muna son ta zamo kamar kasuwanci, ba wai ni na ko yaya, a’a har jikoki suzo su samu kungiyar kwallon kafa ta Kaduna. Misali kamar yadda muke gani ni dan AC Milan ne zaka ga ana Sanya mana shekarun 1908 ko irin su kulab din Asenal, to ta yaya suka dade wa ba kamar a kasar nan ba, don haka muke kokarin samar da kungiyar kwallon kafa ta Kaduna Sabuwa mai inganci har ma a yanzu muna samun goyon baya ga hukumar wasannin Jihar Kaduna da Gwamnan Jihar Kaduna, don haka mu da aka bamu Amanar wannan aiki muna kan yin hakan”.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.