Home / Labarai /  ZA A YI MURNA DA FARIN CIKI DA SALON MULKIN GWAMNA UBA SANI – Ahmad Maiyaki

 ZA A YI MURNA DA FARIN CIKI DA SALON MULKIN GWAMNA UBA SANI – Ahmad Maiyaki

 

Daga Imrana Abdullahi

Wani jigo shugaban al’umma a Jihar kaduna Alhaji Ahmed Maiyaki, ya tabbatarwa da daukacin al’ummar arewacin Nijeriya da cewa kowa zai amfana da salon jagorancin da zababben Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani zai yi a Jihar kowa zai yi Dariya.

Alhaji Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan a Kaduna ya ce hakika ya na bayar da tabbacin cewa jagorancin da Sanata Uba Sani zai yi alkairi ne mai dimbin yawa.

A lokacin wata ganawar da manema labarai domin yin fatan alkairi da murna ga sabon Gwamnan na Jihar Kaduna.

“Kasancewar Sanata Iba Sani a matsayin kwararre da ya kware a fannonin gudanar da ayyuka da kuma rayuwa daban daban zai yi amfani da hakan domin kawo wa Jihar ci gaban da kowa zai amfana, ko a zaman Sanata Uba, a majalisar Dattawan Nijeriya ya gabatar da Kudirori har 32 domin amfanin kasa da jama’ar baki daya, alamce da ke nuni da cewa akwai ci gaba kwarai a jihar”, inji Maiyaki.
“Tabbas hakika Uba Sani zai ɗora bisa kyawawan ayyukan da El-Rufa’i ya yi, da yin gyara a inda aka samu kuskure domin ciyar da jihar Kaduna gaba.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.