Home / Labarai / Za Mu Inganta Harkar Karatun Almajiranci – Shaikh Abdulrahman
Wannan a lokacin da aka Karrama babban mai ba Gwamnan Jihar Kaduna sanata Uba Sani shawara a kan al'amuran addini Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman lokacin da ya karbi lambar karramawar daga Arewa Publishers Forum

Za Mu Inganta Harkar Karatun Almajiranci – Shaikh Abdulrahman

Daga Imrana Abdullahi
Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya jaddada manufa da kudirin Gwamnatin na taimakawa harkar al’majiranci domin samun ingantaccen ci gaban da ake bukata wajen gina al’umma, domin za mu mayar da komai ya zamo dai dai da zamani a samu ingantaccen ilimi.
Babban mataimakin na musamman ga Gwamna ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya karbi lambar karramawa daga kungiyar mawallafan jaridu ta Arewacin Najeriya (Arewa Publishers Forum) karkashin jagorancin Sani Muhammad Garba.
Babban mataimakin ga Gwamnan Jihar Kaduna Abdulrahman Zakariyya Usman, ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta Sanya batun zaman lafiya da hadin kan Juna ne musamman ga kungiyoyin addini ta Sanya a gaba.
“Ina tabbatarwa kowa da cewa Gwamnatin Uba Sani ta hanyar ofishina na mai bashi shawara a kan harkokin addinin Musulunci za mu yi tafiya da kowace kungiyar addini har wadanda ma ba su da wani addini ba tare da wani bambanci ba
“Ba Gwamnatin da za ta zura idanu kawai ta na kallon al’umma ba tare da yin abin da zai ciyar da su gaba ba, hakan ya sa Gwamantin Uba Sani na da cikakken Sani da shirin da za ta dubi wannan harka sosai da nufin a samu ci gaba danga ne da wannan hanya ta Almajiri domin hanya ce ta Koyar da karatun Alkur’ani kuma hanya ce da duk wani gyara da garambawul da ake nufi lallai za a samar da shi cikin hukuncin Allah ba tare da an tsangwami kowa ba ko sanya jama’ a a cikin wata damuwa ba”.
Ya kuma yi kira ga sauran mabiya addinai da cewa hakika Gwannatin Malam Uba Sani Gwamnati ce da ke neman hadin kan al’umma domin babu Gwamnatin da za ta ci gaba idan al’ummarta ba su hada kai ba.
“Domin babu wanda zai kawo hannun jari ko duk wata dukiyarsa idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda haka ne wannan Gwannatin a duk tsakanin kungiyoyi babu abin da take fata da ya wuce hadin kai da tunanin yadda za a ciyar da kasa gaba a kuma yada batun zaman lafiya a tsakanin al’umma, wannan shi ne babban fata na mai girma Gwamna da Gwamnatinsa mai albarka da yardar Allah”.
Ina kuma yin godiya kwarai da wannan karramawar da aka yi Mani Allah ya saka da alkairi

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.