Daga Dan Kaduna Abdullahi
Kwamishinan kula da ma’aikatar ilimin Jihar Kaduna Dakta Shehu Muhammad ya bayyana cewa za a gina ingantaccen dakin rainon yara a makarantar sakandare ta Kawo cikin garin kaduna.
Kwamishina shehu Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da shi da tawagarsa suka kai ziyarar gani da ido yadda harkokin koyarwa da kuma yadda yara dalibai suka dawo makaranta tun bayan dawowa daga hutu a jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da babban dalilin da yasa za a gina wannan dakin rainon yara shi ne saboda irin yadda mata malamai suke da yawa da suka kai shittin (60) a wannan makaranta, saboda idan an gina wannan dakin raino zai ba malaman mata damar su gudanar da aikinsu na koyar da dalibai kamar yadda ya dace.
Ya kuma ce za a gina karin Ajujuwa da Ban dakuna domin zagaya wa ga duk masu bukatar yin haka a makarantar.
Duk da kamar yadda Kwamishinan ilimin ya bayyana cewa dalibai sun dawo a kan Kari, ya kuma yi kira ga iyayen yara da su kokarta domin ganin yayansu sun dawo makarantar saboda lokacin karatu ba zai jira kowa ba.
Ko a cikin wata sanarwar da ma aikatar ilimin Jihar karkashin jagorancin Dakta Shehu Muhammad ta bayyana cewa za a hukunta masu kunnen kashin da suka kasa dawowa makaranta a kan kari.