Home / Labarai / Zan Sauka Daga Gwamnan Zamfara – Bello Matawalle

Zan Sauka Daga Gwamnan Zamfara – Bello Matawalle

Zan Sauka Daga Gwamnan Zamfara – Bello Matawalle
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Muhamamdu Bello (matawallen Maradun) ya bayyana cewa a shirye yake ya sauka daga kujerar Gwamnan Jihar Zamfara in dai za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya mutanen Jihar su ci gaba da walwala kamar kowa.
Gwamna Bello Matawalle ya ce hakika yana son zaman lafiya da ci gaba tare da karuwar arzikin al’ummar Jihar Zamfara baki daya saboda haka “in za a samu zaman lafiya mutanen Jihar Zamfara su kwanta su yi Bacci da idanunsu biyu a rufe, su gudanar da harkokinsu kamar yadda kowa yake bukata tare da walwala, ni zan iya sauka in ajiye Gwamnan Jihar Zamfara domin ba wai ina son yin Gwamna ba ne ta kowace hanya ko yin mulki a mutu ko ayi rai ba”. Inji shi.
Ya kara da cewa shi baya goyon bayan matakin da Gwamnatin tarayya ta dauka na hana Jirgin sama zuwa Jihar, saboda tun lokacin da shi da kansa ya jagoranci kama mutanen da suke harkar hakar ma’adinai a kwanan baya har yanzu babu wani lamari mai kama da hakan ba bisa ka’ida ba.
“Kuma ai Gwamnatin Jiha ba ita ce ke bayar da lasisin ginar ma’adinai ba, Gwamnatin tarayya ce kuma akwai babban jami’in Gwamnatin tarayya mai kula da wannan aiki to, ta yaya za a zauna a yanke irin wannan hukunci”.
Ya ci gaba da cewa “mamata ya yi a zauna tsakaninsu a samo matsayar da ya dace a cimma, lokacin da majalisar kula da tattalin arzikin kasa da kuma majalisar Zartaswa su duba yanayin Jihar Zamfara kasancewarta mai dimbin arziki”.
Duk mutanen da aka kama a kwanan baya yan kasashen waje duk an kai wa shugaban Yan Sanda su a Abuja kuma “ni na jagoranci hakan don haka ba wani abin boyo a lamarin, to yanzu ta yaya za a kalli Jihar a idanun duniya bisa wannan matakin da aka dauka?.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.