Home / Labarai / Zanga – Zanga Ba Abin Alkairi Bace- Bashir Nafaru

Zanga – Zanga Ba Abin Alkairi Bace- Bashir Nafaru

An bayyana batun Zanga Zangar da wadansu mutane ke kokarin shiryawa a Majeriya da cewa abu ne da ba abin alkairi ba Honarabul Bashir Nafaru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu.

Bashir Nafaru ya ci gaba da cewa duk wani mai son abin alkairi da kishin Najeriya zai san lallai yin Zanga Zanga ba abin alkairi bane a kasa Najeriya domin yin Zanga Zanga zai iya haifar da komai a wannan kasa mai albarka.

A saboda haka ne muke yin kira ga tsofaffi, iyaye da Kakannin my da su tashi tsaye wajen yin addu’a a wannan kasa, da nufin Allah ya albarkace ta ya sa duk tsananin da ake ciki ya dawo mana abin alkairi ya zamanto kasar ta ci gaba da zama hamshakiyar kasa a tsarin Dimokuradiyya, Allah muke roko ya shirya mu da iyayen mu baki daya”.

A game da batun kowace karamar hukuma ta samu yancin kanta kuwa, hakika hakan ya haifarwa kasar samun yan takarar shugabannin kananan hukumomi da kowa ke son ace shi ne shugaban karamar hukuma ya samu Garabasa a kauyensu ko a kananan hukumomin su.

“A Sani fa cewa karamar hukuma wuri ne da ake samun hakkokin jama’a idan mutum ya kwashe dukiyar jama’a ko dai ya ci kudin ya na da rayuwa ko kuma bayan ran mutum wanda ana iya samun mutum ya koma a kan motoci ko Babura har ma da Kekuna saboda kudin Talakawa ne da aka yi ruf da ciki da su ya dace mutum fa ya tabbata lamarin na jiran ka ko mutum ya ta fi lahira don haka ya dace kowa ya ji tausayin al’ummar sa da nufin samun ci gaba”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.