Home / Labarai / Zulum Na Kokarin Gano Sansanoni Da Yan Gudunhijira Na Karya

Zulum Na Kokarin Gano Sansanoni Da Yan Gudunhijira Na Karya

Zulum Na Kokarin Gano Sansanonin Karya
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an tsaftace batun sansanonin yan gudunhijira Gwamnan Babagana Umara Zulum ya ziyarci sansanonin domin tabbatar da yawansu.
Gwamnan ya kuma tabbatar da samun wadansu na Bogi dari 650.
Da tsakar Daren ranar Lahadi ne, Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci kwalejin Koyar da ilimin addinin Islama ta M9hammed Goni da ke Maiduguri, wurin da aka ajiye yan Gudunhijira daga karamar hukumar  Abadam arewacin Borno.
Gwamna Zulum nan da nan ya rufe Kofar shiga sansanin ya kuma rika Sanya idanu wajen kidayar mutanen da ke cikin sansanin domin yin maganin yawaitar samun yan Gudunhijira na karya da ke Damfara da sunan su yan Gudunhijira ne da suke zuwa sansanin domin kawai su cinye abincin yan Gudunhijirar sai idan Dare ya yi su koma gidajensu.
Duk da irin kokarin da Gwamnatin ke yi wajen samawa marasa karfi abinci da abin yi da suka kasance ba yan Gudunhijira ba.
Gwamnan wanda ya kai har karfe daya na safe, ya gano cewa daga cikin mutane 1000 a yanki yankin yan Gudunhijira dari 650 duk na Bogi ne.
An samu gida ko yanki yankin wurin da yan Gudunhijira suke guda dari 450 wanda an tabbatar yan Gudunhijira ne na gaske bayan kammala kidayar da aka yi da tsakar Dare wanda Gwamnan tare da jami’an hukumar bayar da tallafin gaggawa ta kasa NEMA suka yi tare da babban sojan Sama M. T. Abdullahi,kwamishinoni huda biyu na ( aikin Gona da kwamishinan kula da kananan hukumomi da masarautun gargajiya).
A tsarin harkar jinkai, ana samun wurin zama guda daya a sansanin yan Gudunhijira a samu mutane shida (6) ko dai suna da dangantaka ta hanyar iyali ko kuma sun zabi su zauna tare domin su rika karbar abin tallafin da ake raba masu.
Jami’an da aka yi wannan kidayar da su sun tabbatar da cewa Gwamna Zulum bai taba nuna jan kafa ba wajen amincewa da duk abin da za a ba yan gudunhijirar da ke bukatar abincin da za su ci.
Sai dai Gwamnan baya bukatar a rika samun wasu mutanen da suke zuwa sansanin suna Karbe abincin da ake ba wadansu su ne asalin yan Gudunhijira kuma suna amfana da shirye shiryen da ake ba mutanen da ba a sansanin Gudunhijira suke ba.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.