Home / Labarai / An Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iayayensu

An Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iayayensu

An Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iayayensu
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda bayani ya gabata a tun shekaran jiya cewa cikin hukuncin Allah daliban makarantar Koyar da aikin Gona da al’amuran Gandun daji sun samu kubuta daga hannun yan bindigar da suka sace su a wani Dare cikin harabar makarantar da ke Unguwar Afaka karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Kamar yadda zaku iya gani a cikin hoton nan daliban ne a cikin ingantattun kaya masu kyau da tsada wasu na ta kuka domin murnar sake haduwa da iyaye da yan uwa tun bayan da aka sace su a cikin makarantar inda suka kwashe tsawon kusan watanni biyu a hannun yan bindiga a cikin daji.
Daliban dai sun yi bayanin cewa tsawon zamansu a wurin yan bindigar ana ba su Tuwo miyar kuka sau daya a rana inda suka tabbatarwa manema labarai cewa babu dai maganar ingantaccen abinci ko kadan.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan mika daliban ga iyayensu yan uwa da abokan arziki Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan, bayyana godiyarsa ya yi da nasarar kubutar da daliban, inda ya kara tabbatarwa da jama’a cewa Gwamnati na iyakar bakin kokarinta domin kawo karshen ayyukan yan bindiga da sauran makamantansu.
Kwamishinan yan Sanda na Jihar Kaduna Umar Muri cewa ya yi suna nan su na kokarin kubutar da daliban jami’ar Greenfield mai zaman kanta da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kuma ya ce za a samu nasarar da ake bukata in Allah ya amince.
Shugaban makarantar koyon aikin Gona da Gandun daji Dokta Bello Mohammed  Usman cewa ya yi suna murna da farin cikin sake hada dalibai da iyayensu kuma nan gaba kadan za a ci gaba da gudanar da aiki kamar yadda aka saba a cikin makarantar.
“Nan gaba kadan dalibai za su rubuta jarabawarsu saboda daman sun kusa fara jarabawa ne wannan al’amari ya faru”, inji shi.
A wurin taron mika wa iyaye yayansu tun bayan da yan bindigar suka sace su, taron da aka yi a dakin taro na makarantar da ke Afaka ya samu halartar yan uwa da abokan arziki wasu na kuka, wasu kuma na rawa su na murnar sake haduwa tun tsawon kusan watanni biyu da yan bindiga suka sace su.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.