Home / News / GWAMNATIN JIGAWA ZATA KASHE BILLION N12.1 A HARKAR NOMA

GWAMNATIN JIGAWA ZATA KASHE BILLION N12.1 A HARKAR NOMA

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ware kudi kimanin Naira biliyan dubu N12.1 domin a kashe su a fanin aikin Gona a cikin kasafin kudi na shekarar 2021, wanda ya gabatar kwananan a gaban zauren majalisar Jiha.
Gwamnan ya ce “Wannan wata hanyace ta samar da ci gaban tattalin arziki wacce za ta samar da wadataccen abinci da dunbin ayyukan yi.”
Ya kara da cewa samar da sama da naira biliyan goma sha biyu da miliyan daya, zai bunkasa samar da abinci ta hanyar sabbin dabarun noma da Karin gonakin noma.
A cewar sa, daidaikun manoma da kungiyoyi da masu kanana da matsakaitan sana’o’i zasu samu tallafin bunkasa sanao insu domin samun nasarar da ake bukata.
Hakazalika, Ayyukan cigaba da bankin musulunci ya fito dasu domin bunkasa tsarin noman rani guda goma sha tara da muke dasu, zai shafi kimanin  kadada  dubu uku da dari biyu a fadin jihar nan.
Irin wannan tsare-tsare da tallafi zai samar da dunbin ayyukan dogaro da kai da kyautata rayuwar  mutane da iyalansu.
Auwal D Sankara (FICA)
Senior Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Babban Mataimaki na Musamman Ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafan sadarwa)

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.