Home / News / Yadda Ake Noman Waken Soya

Yadda Ake Noman Waken Soya

Yadda Ake Noman Waken Soya
Daga Umar Ahmad Unguwar Buhari
Kamar dai yadda masu karanta wannan jarida ta theshieldg.com mai wallafa labarai tare da makaloli a yanar Gizo suka bukata na sanin yadda ake Noman Waken Soya, musamman a yanzu da ya kasance a sahun gaba bangaren amfanin Gona da kamfanoni da kuma jama’a suke sarrafawa  domin amfanin yau da kullum, ya sa wani matashi manomi da ya kammala karatun jami’a kwanan nan Malam Umar Ahmad da ake wa lakabi da “Babangida” Unguwar Buhari gundumar Magajin Makera a karamar hukumar Funtuwa cikin Jihar Katsina ya rubuto mana yadda ake Noman waken Soya kamar haka.
Ya dai fara ne da irin yadda ake farawa tun daga sharar Gona tun da farkon bazata kafin ruwa ya zuba,Yadda ake noman waken Soya kuma shi ne.
Kuma za a iya yin amfani da Takin zamani kamar kamfa, a wajen fara shuka a Sanya shi kadan cikin irin shuka a shuka tare da shi ko kuma a bari sai lokacin da aka yi masa Noman farko a dan diga kadan. Ko kuma ana iya Sanya wa a lokacin da za a yi hudar karshe, a wannan lokacin ana iya yin amfani da Takin zamani na yuriya saboda Waken Soyar ya yi kwari sosai
Duk Gonar da aka sanyawa Takin gargajiya na Bola ko kashin Dabbobi hakika za a ga amfanin Gona kamar yadda ake bukatar a samu.
Amma idan za a yi amfani da Takin zamani kadan kadan ake sanyawa domin shi Waken Soya haka yake bukata.
 Idan Gonar da za’a shuka shi  hura ce wato shekarar da ta gabata ( an yi masara) to zai fi kyau fiye da ace Waken Soya aka yi a shekarar da ta gabata wato dai bayason a zamanto a maimaita shuka shi a Gona daya a shekara daya da ta biyu a Jere.
Sai a samu lafiyayyen iri, Sannan a share Gonar sosai kuma shara mai kyau, Sannan ajira zubar ruwan sama.
 Idan ana son ya yi nagari to za’a nemo Takin kashin kaji azo ran da za’a yi hudar shukan sai a watsashi kafin shukar sannan sai huda sai shuka.
Amma fa shukar Waken Soya dole sai an samu wadanda suka iya shukar domin shi ba kamar Masara ba ne ko yadda ake Shuka Dawa, saboda shi baya son a cika tura masa kasa a kansa a taka sawun shuka da karfi ya danne shi, saboda kamar yadda aka san yanayin wake yake in an danne shi da kasa matsala yake bayarwa.
Idan anason yai aukin cika buhu sai ashukavshi zalla ko a saka giccin Dawa ko Masara kadan kadan idan aka yawaita Dawa ta na hana shi yin yadda yakamata.
Bayan shuka idan ya gama fita ya fara girma za’a yi masa noma da ciro abarshi uku-uku ko hudu-hudu, in kuma Gona mai nagari ce ma ko ba a yi masa ciro ba ya na bayar da abin da ake bukatar a samu.
Da ganan za’a jira zuwa lokacin turi Sato (huda ta biyu)
Bayan nan sai a jira zuwa lokacin ya nuna za a ga ganyensa ya fara canzawa ya na yin ja da haka da haka har ya kakkabe ganyen da ke jikinsa, duk jikinsa tare da kwayoyin Waken duk su bushe sai a nemo masana Noman Waken Soya su bayar da shawarar lokacin da ya dace a cire shi domin ba a barinsa ya kammala bushewa baki daya ba a Tuge shi ba aka tara a wuri daya domin gudun kada ya kakkabe.
 Bayan an tara shi wuri daya in kuma yana da yawa sai ayi masa tari tari domin ya sha Iska aji dadin buge shi a dura a buhuna.
Sannan akwai yanayi ma’ana idan ba ka da karfin saka kashin kajin ba dole ba ne amma sawar ya fi
Sai kuma wani karin gyaran Gona idan da hali shi ne ayi mata haro bayan zubar ruwan sama sau biyu ko uku wato dai idan Gona ta jika sosai da ruwan sama.
Umar Ahmad Unguwar Buhari Makera Funtuwa ne ya rubuto wannan Makalar.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.