Home / Labarai / Mutane Na Biyayya Ga Dokar Hana Fita A Kaduna

Mutane Na Biyayya Ga Dokar Hana Fita A Kaduna

Daga I  Abdullahi Kaduna
Tun bayan da a jiya Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i da ta Sanya dokar hana fita tsawon Awa Ashirin da Hudu wato Dare da rana kenan a kokarinta na ganin an yi yaki da cutar Covid- 19 da ake kira da Korona bairus.
A yau da wakilinmu ya zagaya cikin garin kaduna domin ganawa idanunsa yadda lamarin ya gudana ya fahimci cewa mutane sun yi biyayya kwarai a game da bin dokar domin a kan tituna zaka ga ba kowa sai shingayen jami’an tsaro a wuraren da suka kafa su.
Sai kuma masu ayyukan musamman da ke aiki kamar yadda tsarin ya tanadar.
Da wakilinmu ya zagaya kan titin bayan gari na Yamma inda aka sanar cewa masu son wucewa da suka fito daga wadansu wurare ko Jihohi za su iya bi domin su wuce, ya ga irin yadda ake samun Tururuwar jerin Gwanon motoci masu son wucewa zuwa wadansu Jihohin na daban.
Sannan a tashar motar Kawo ma da ke cikin garin Kaduna mutane na nan Tankam da jakunkunansu suns son ficewa daga garin kaduna zuwa wuraren da suka nufa.
Sai dai kamar yadda wakilin namu ya ganawa idanunsa kamfanin Mother cat da yake aikin shimfida titi a yankin kawo da za a yi amfani da shi idan za a yi aikin Gadar Kawo da Gwamnati ta bayar da aikin budewa da tsawaita gadar nan kamfanin na gudanar da aikinsa a yau Juma’a 27 ha watan uku na Maris 2020, wato ranar farko da aka kafa dokar hana fita ba dare ba rana.
Sai kuma a cikin unguwanni suna tafiyar da harkokinsu lafiya kalau kamar yadda suke gudanarwa a kullum.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.