Home / News / 2023: Dokta Harris Jibril Mukeson Ya Tsaya Takarar Gwmanan Jihar Kaduna

2023: Dokta Harris Jibril Mukeson Ya Tsaya Takarar Gwmanan Jihar Kaduna

Daga Wakilin mu A Jihar Kaduna
Shugaban Kungiyar Harris Support Organization (HSO) ta kasa, Umar Faruk Magume yace bisa la’akari da kasancewar Jihar Kaduna cibiyar ilmi da wayewa a Najeriya, kuma cibiyar arewacin Najeriya, ya cancanci a ce wanda zai gaji mulkin jihar ya zama haziqin nutum mai fasaha, sannan masanin harkokin siyasa da tattalin arziqi.
Magume, wanda tsohon xan takarar Xan Majalisar Jihar Kaduna ne a mazabar Wajen Zaria, ya bayyana haka ne a cikin takardar da ya rattabawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a garin Kaduna, inda yace bisa dogaro da hakan ne ta sa suka yanke shawarar yin kira ga dan siyasar akida irinsu Dakta Harris Jibril da ya fito don neman mulkin jihar a zaben 2023 saboda cancantarsa da kuma qwarewarsa kan sha’anin tattalin arziqi da siyasa da kuma hangen nesa.
“Kowacce al’umma tana dogaro ne da tattalin arziki ko qirqiro ababen more rayuwa. Sannan al’umma suna buqatar shugaba ne mai hangen nesa da samar da ayyukan yi ga al’umma tare da bunqasa ilmi tun daga tushe. Waxannan siffofin duka Injiniya Dakta Harris HM Jibril ya tattaro su.” Inji shi
Yace sun kafa qungiya ne don yin kira ga Dr Harris kan tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna bisa ga hidimtawa al’umma musamman matasa a matakai daban daban.
“Don haka yasa Harris Support Organization da haxin gwiwar gamayyar qungiyoyin mata da matasa, suka ga ya cancanta daya fito ya ceci jihar Kaduna yayi takaran gwamna a shekarar 2023.” Inji sanarwar
Dakta Harris Jibril ya rike shugaban jam’iyyar ADP a Jihar Kaduna a shekarar dubu biyu a shekarar (2018),  sannan ya fito takarar Sanata a Shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zaben 2019 karkashin inuwar jam’iyyar PRP, kuma a yanzu haka shine shugaban Majalisar Tuntuba da Hadaka ta Arewa (Arewa Consultative and Synergy Congress-ACSC) na kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.