Home / News / AMINU MAKETA MAI HOTO BIRNIN GWARI YA KONA HOTUNAN YAN TAKARAR PDP DA YAKE DAUKE DA SU

AMINU MAKETA MAI HOTO BIRNIN GWARI YA KONA HOTUNAN YAN TAKARAR PDP DA YAKE DAUKE DA SU

….YA CANZA SHEKA ZUWA APC SABODA KAUNAR GWAMNA MATAWALLE NA ZAMFARA
DAGA IMRANA ABDULLAHI
SAKAMAKON tsananin kauna da Soyayya da  mutumin da ake yi wa lakabi da Maketa Mai Hotunan tallar jam’iyyar PDP a cikin garin Kaduna da Jihar baki daya saboda tsananin Kaunar Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Muhammad Bello Matawalle nan take ya canza sheka zuwa APC domin tallata jam’iyyar APC baki daya.
Kamar yadda aka San shi da sunan Mai dubun tsumma da wasu ke ce masa Maketa Mai hoto da ya yi shekaru Goma sha Bakwai ya na tallar PDP da dukkan yan takarar ta a kowane irin mataki ya canza sheka zuwa tallar jam’iyyar APC.
Maketa Mai hoto ya shaidawa dimbin jama’a lokacin da yake Kona fastocin yan takarar PDP da suka hada tun daga mai takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da mataimakinsa da sauran masu yin takara a jam’iyyar a matakai daban daban, amma a yanzu na canza sheka na bar tallar yayan PDP sai tallar Dodo kawai ba wata magana.
“Hakika ban ya ba ganin wannan mutumin ba da ake kira Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, amma kuma ya taimaka Mani domin in daina wahala, ni Aminu Maketa Mai hoto na Birnin Gwari a halin yanzu an ba ni kyautar mota da gida domin kamar yadda Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya alkawarta Mani cewa gobe in zo in karba kuma zai kai ni ga Gwamnan Jihar Zamfara domin mu gana ido da ido”, inji Aminu Maketa mai hoton PDP a da can.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara ne a kan harkokin hulda da kasashen waje da kuma kungiyoyi ya ce dukkan kokarin da yake yi wajen wannan bawan Allah Aminu Maketa mai hoto ya dawo APC ya na yi ne domin Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle da aka ba shi jagorancin wannan shiyyar Arewa maso Yamma domin tabbatar da samun nasarar APC a shiyyar da kasa baki daya”.
A take jama’a da dama suka zuwa suna yi wa Sarkin Shanun Shinkafi na farko Dokta Suleiman Shu’aibu godiya bisa wannan kokarin da ya yi na canza Aminu Maketa Mai hoto zuwa APC bayan duk ya cire dukkan hotunan yan takarar PDP tun daga na shugaban kasa zuwa har na yan majalisu baki daya.
A ta bakin wani mutum ” mun dade muna kokarin jan hankalinsa da ya rabu da wannan wahalar tallar yan takarar PDP da ba su bashi komai, amma wallahi yaki sai ga shi a yanzu ake gaya mana cewa akwai wani da ya Sanya shi ya bar tallar ya kuma cire dukkan hotunan yan takarar baki daya, hakika muna godiya kwarai da wannan mu mutanen APC ne a Jihar Kaduna”.
Sakamakon irin wannan alkawarin da aka yi wa Aminu Maketa mai tallar yan takarar PDP a kan Babur dinsa tsawon shekaru 17 tun zamanin mulkin tsohon Gwamna Muhammad Makarfi a Kaduna nake tallar yan takara nan, nan take sai Aminu Mai hoto ya fashe da kuka ya na cewa sai Dodo, wato Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawalle zan zabi APC Bola Ahmad Tinubu da sauran yan takara baki daya domin na koma APC kawai ba wata tantama.
Shi dai Aminu Maketa Mai hoto Birnin Gwari mutum ne sananne a cikin garin Kaduna da Jihar baki daya saboda irin yadda yake tallata PDP da yan takarar baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.