Home / Kasashen Waje / KADA WANI DAN NIJAR YA SHIGA HARKOKIN SIYASAR NAJERIYA – DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM

KADA WANI DAN NIJAR YA SHIGA HARKOKIN SIYASAR NAJERIYA – DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad shugabar kungiyar A A Charity Foundation ta yi kira ga daukacin al’ummar kasar Nijar mazauna Najeriya da kada su sake su saka kansu a harkokin siyasar Najeriya.

Dokta Aminatou ta yi wannan ne a cikin wani sakon murya da ta aikewa al’ummar Nijar mazaunan Najeriya da ta ce kasar yan Nijar ce ta biyu don haka sai a ci gaba da yin fatan alkairi da kokarin da kasar take yi domin gudanar da zaben ta za a yi a Najeriya.

“Kada wani dan Nijar ya shiga cikin harkokin zaben Najeriya, abin da kawai za a yi shi ne fatan alkairi kada kowa ya shiga cikin harkokin zaben Najeriya, muna zaune ne a Najeriya matsayin kasa ta biyu amma kada wanda ya shiga cikin harkokin zaben da ake yi yanzu”.

Dokta ta ci gaba da cewa “ina kira ga kowa ya kama jikinsa ya zauna a cikin gidansa kada kowa ya shiga cikin zaben Najeriya, mu yi Najeriya addu’a mazaunin kasar mu ta biyu da muke zaune a cikinta, zaben da ya tunkaro Allah ya sa a yi shi lafiya a gama lafiya ya kuma Zabar mana shugabanni nagari, ayi lafiya a kammala zaben lafiya, Allah ya kara hada kanmu da fatan alkairi”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.