Home / Labarai / AKWAI BUKATAR YIN CANJI A JIHAR ZAMFARA – NA FARU

AKWAI BUKATAR YIN CANJI A JIHAR ZAMFARA – NA FARU

Daga Imrana Abdullahi

An bayyana Jihar Zamfara a matsayin wurin da ake bukatar samun canji domin al’amura su ci gaba da inganta.

Dan takarar kujerar majalisar wakilai a kananan hukumomin Anka da Talatar Mafara karkashin jam’iyyar ADC, Alhaji Bashir Nafaru ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai garin Talatar Mafara.

Bashir Nafaru ya ce hakika a game da zabe ana bukatar a samu canji domin “wadanda ke kan mulkin ba su yi wa kowa adalci ba kuma a koda yaushe jama’a na bukatar ayi masu adalci ta yadda kowa zai samu rayuwarsa ta inganta”.

Bashir Nafaru ya ci gaba da bayanin cewa “akwai bukatar ayi zaben Wake da Shinkafa har da miya domin ta haka ne jama’a za su samu adalcin da ake bukata, yin hakan zai sa yan siyasa su tashi tsaye wajen taimakon al’umma”.

Na Faru ya kuma yabawa hukumar zabe ta kasa da ta shirya zaben da ya gudana inda aka zabi shugaban kasa da yan majalisar Wakilai da tarayya.

“Lallai hakika kamar yan Siyasar Jihar Zanfara idan ba a yin zaben Wake da Shinkafa sai kowa ya yi kwanciyatai kawai, amma da zarar ana yin irin wannan zabe yadda hukumar zaben ta shirya shi kowa sai ya tashi tsaye.

Bashir ya kuma yabawa hukumar zabe bisa irin yadda ya shirya zaben da ya gudana.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.