Home / News / APC TA LASHE ZABEN MAZABAR FUNTUWA DA DANDUME

APC TA LASHE ZABEN MAZABAR FUNTUWA DA DANDUME

Daga Imrana Abdullahi

Kasancewar an gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya da na Dattawa a tarayyar Najeriya tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekaru 23 da suka gabata a halin yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta aiwatar da zaben sun fara sanar da wasu zabukan, hakan ya sa hukumar ta sanar da sakamakon zaben mazabar dan majalisar Funtuwa da Dandume.

Kamar dai yadda hukumar ta sanar ya nuna cewa APC ta lashe zaɓen mazaɓar Funtua/Dandume

Barista Abubakar Mohammed Ahmad Gardi na jam’iyyar APC ya lashe zaben dan majalisar tarayya ta mazabar Funtua/Dandume.

Barista Mohammad Ahmad ya doke Honorable Abubakar Salisu ASAS na jam’iyyar PDP da sauran ƴan takarar.

 

Ga dai yadda sakamakon zaben ya kasance a  Mazabar Funtua da Dandume

APC – 23,901

PDP – 14947

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.