Daga IMRANA ABDULLAHI
Bayanan da muka samu a halin yanzu na cewa Allah ya yi wa Mahaifiyar sanannen Malamin nan da ke Kaduna Shaikh Ahmad Abubakar Gumi rasuwa.
Malam Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ne da kansa ya sanar da rasuwar Mahaifiyar tasa da Yammacin ranar Lahadi.
Bayanan da muka samu na cewa Mahaifiyar Dokta Gumi ta rasu ne a yau Lahadi da misalin karfe 5: 30 kuma za a yi Jana’izarta a kuma Kaita makwancinta da ke makabartar Unguwar Sarki a cikin garin Kaduna.
A cikin wata sanarwar da aka wallafa a shafinsa na Fezbuk Malamin addinin musuluncin ya ce
“Inna lillahi WA inna ilaihi rajiun.Ga Allah muka fito kuma a gare shi zamu koma yau da misalin karfe 5: 30, ina sanar da ku tare da bacin ciki cewa mahaifiya ta ta rasu.
“Don haka ku yi mata addu’ar neman gafarar Ubangiji Allah madaukakin Sarki ya gafarta mata, Allah kuma ya Sanya ta da dukkan yayanta da jikinta a cikin Aljannah madaukakiya