Bayanan da muke samu na cewa a kalla Gawarwaki Goma (10) ne aka gano bayan da yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari a Unguwar Wakili da ke karamar hukumar Zangon Kataf cikin Jihar Kaduna,a Daren Jiya.
Sai dai a cikin wata takardar da aka fitar mai dauke da sa hannun Yabo Chris Ephraim, mataimaki na musamman a kan harkokin yada labarai ga shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, ta bayyana cewa tuni aka Sanya dokar haka fita tsawon Awa Ashirin da hudu “24” a unguwannin Juju, Mabuhu, Unguwar Wakili da kuma Zango urban nan take.
An kuma yi hakan ne kamar yadda takardar ke cewa domin a ba jami’an sojan Najeriya su yi aikin dawo wa da doka da oda a wannan wurin.