Home / Big News / Kotun Koli Ta Tabbatar Da Dauda Lawal A Matsayin Dan takarar Gwamnan PDP A Jihar Zamfara

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Dauda Lawal A Matsayin Dan takarar Gwamnan PDP A Jihar Zamfara

 

Kotun Koli a tarayyar Najeriy ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar Gwamna karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara.

Wannan tabbatacciyar magana ta zo ne a ranar sati,domin gudanar da zaben Gwamnoni a ranar 18 ga watan Maris kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana.

A wani hukuncin bai daya da alkalan su biyar baki daya suka amince da shi inda suka yi watsi da wata bukatar da aka kawo ta na a amince da wani dan takarar Gwamna, Dokta Ibrahim Gusau.

 

A hukuncin da jagoran alkalan Alkali Adamu Jauro ya karanto, cewa kotun kolin ta amince da abin da lauyan Dauda Lawal, Damina Dodo,ya gabatar mata cewa wanda yake tsayawa ne sahihin dan takara da aka zaba ya hanyar halak domin an bi tanajin doka kamar yadda ta tsara.

Alkali Jauro ya bayyana cewa sun tabbatar da hukuncin daukaka kara ta Sakkwato, da a ranar 6 ga watan Janairu Janairu wannan shekarar, kotun ta amince da yadda aka yi zaben fitar da dan takarar a karo na biyu, wanda Dauda Lawal ya samu nasara.

Dauda Lawal a zaben fitar da dan takarar ya samu kuri’u dari 442 wanda ya bashi nasarar zama dan takara da ya kayar da Dokta Ibrahim Gusau da sauran wadansu yan takarar.

Alkali Jauro ya kuma tabbatar da cewa babbar kotun tarayya da ke Gusau da ta rushe zaben fitar da dan takarar har sau biyu ba ta da hurumi a lokacin da Dokta Gusau ya shigar da kara.

Kotun daukaka kara da ke yankin Sakkwato a 6 ga watan Janairu ta amince da zaben fitar da dan takarar da ya fitar da Dauda Lawal, a matsayin dan takarar Gwamna a  jam’iyyar PDP domin zaben Gwamna a ranar 11 ga watan Maris, 2023, a Jihar Zamfara.

 

Zaben fitar da dan takarar Gwamna na farko an yi shi ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2022, amma an kalubalanci hakan a babbar kotun tarayya da ke Gusau kuma ta rushe zaben.

 

Babbar kotun tarayyar a hukuncin da ta yanke ta ce ne a sake yin zaben fitar da dan takara kuma an aiwatar da hakan wato sake zaben a ranar 23, ga watan Satumba 2022, amma kuma ita dai wannan kotun ta sake Sanya alamar tambaya wato ta rushe zaben saboda abin da ta kira kura – kurai da aka yi.

Amma saboda rashin gamsuwa da hukuncin babbar kotun, Dokta Dauda Lawal Dare, Adamu Maina Waziri, wanda shi ne shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben fitar da dan takarar da Kanar Bala Mande mai ritaya sai suka shigar da kara kotun daukaka kara suna neman tabbatar masu da zaben da suka yi.

About andiya

Check Also

APC National Chairman, Ganduje Commissions Road Named After Him in Gombe

  …Lauds Governor Inuwa’s Examplary Leadership …Says “President Tinubu, APC Leadership Proud of Gombe Governor’s …

Leave a Reply

Your email address will not be published.