….Gobe Juma’a take ranar Sallah
Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Sakkwato na cewa Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Dokta Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan Sallah wanda ya kawo karshen watan Azumin Ramadana da al’ummar musulmi suka yi a wannan shekarar.
Mai alfarma Sarkin musulmin ya sanar da hakan ne a wajen taron manema labarai da ya yi a fadarsa da ke Sakkwato.
Inda ya tabbatar da cewa an ga watan a wurare da dama da Yammacin yau Alhamis.
Saboda haka gobe idan Allah ya kaimu za a yi Sallah kenan a duk fadin tarayyar Najeriya.