Zababben gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa kwamitin mika mulki

Daga Hussaini Yero

Zababben gwamnan Jahar Zamfara Dr Dauda Lawal Dare ya kafa kwamitin amsar mulki daga gwamnatinMuhammadu Bello Matawalle mai manbobi sitin .

Wannan na kushe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun zababen gwamnan wajan yada labarai Sulaiman Bala Idris ya sanyawa hannu a jiya Laraba ya raba wa manema labarai a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Suleman Bala bayyana cewa,kwamitin zayyi aiki ne tare da Kwamitin gwamnatin gwamna Bello Matawalle mai barin gado, gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu. a cikin jihar.

Kuma tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya MD Abubakar CFR ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Dr. Hamza Mohammed zai zama Sakataren Kwamitin.

Har ila yau, kwamitin ya hada da tsohon shugaban ma’aikata na jihar Zamfara, Mujitaba Isah Gusau; Col. Bala Mande (Rtd.); Farfesa Abubakar Aliyu Liman; Barr. Nura Ibrahim Zarumi; Barr. Bello Galadi, da sauransu.

Kwamitin dai ya kunshi manyan mutanan da masu rike da mukaman gwamnati da masu ritaya da kuma kwararru da daga kowane bangare na rayuwa alumma.

Babban aikin kwamitin shi ne samar da tsarin tuntuɓar juna tare da kafa hanyar sadarwa ta yau da kullun tare da gwamnati mai barin gado don amasar mulkin cikin sauƙi.

Bugu da kari, kwamitin zai hada ma’aikatun da ma’aikatu, da hukumomi (MDAs) tare da duba kudaden gwamnati mai barin gado tare da mai da hankali kan kudin shiga, kadarorin Gwamnatin da sauransu.

Nan gaba kadan ne za a bayyana ranar da za a kaddamar da kwamitin mika mulki ga Gwamna.Inji Suleman Bala.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.