Home / News / An Nada Surajo Baba Malumfashi Shugaban Katsina United

An Nada Surajo Baba Malumfashi Shugaban Katsina United

 

Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Katsina na cewa Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya nada Surajo Baba Malumfashi a matsayin shugaban kulab din kwallon kafa na Katsina United.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun M. ONasiru Gide.

Takardar ta ci gaba da bayanin cewa shugaban kulab din mai barin Gado Yarima Abdulsamad Badamasi wanda ya ta fi neman lafiya a halin yanzu ya mika ragamar ne a ta hannun kodineta Janar Alhaji Sani Tunau.
Taron mika ragamar shugabancin kulab din an yi shi ne a dakin taro na Muhammad Dikko sa ke harabar filin wasa na Muhammad Dikko cikin garin Katsina.

Alhaji Surajo Baba Malumfashi ya bayyana kudirinsa na yin aiki tukuru ba tare da gajiyawa  a wajen kara inganta al’amuran kulab din na nufin kai shi babban mataki na gaba da duniya za ta yi alfahari da shi.

Sai ya bukaci da a bashi cikakken hadin kai da goyon baya daga Jagororin da ke tafiyar da kulab din da nufin samun nasara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.