Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga babban birnin tarayyar Najeriya Abuja na cewa Allah ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi rasuwa.
Marigayin dai kamar yadda wata sanarwa ta bayyana cewa ya rasu ne a garin Abuja kuma za a yi Jana’izarsa a babban masallacin Abuja da misalin karfe hudu na Yammacin yau Lahadi bayan an yi Sallar La’asar.
Hakika karamar hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara, Arewacin Najeriya da kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu sun yi babban rashi domin gurbi ne da aka bari mai wuyar cikawa.
Allah ubangiji ya jikansa da rahama yasa mutuwa hutu ce amin summa amin.