Home / Labarai / Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Gwamna Abba Kabir, IG Za su Halarci Bikin karrama ‘yan sanda a Wudil

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Gwamna Abba Kabir, IG Za su Halarci Bikin karrama ‘yan sanda a Wudil

Daga Imrana Abdullahi

A gobe ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Sanata Kashim Shettima zai isa Kano domin halartar bikin yayen daliban makarantar horar da ‘yan sandan Najeriya a Wudil.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a yau.

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne zai tarbi mataimakinsa a filin jirgin sama na Aminu Kano sannan zai wuce wurin da babban sufeton ‘yan sandan kasar Kayode Adeolu Egbetokun wanda tuni yaje Kano domin shirye-shiryen taron.

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai raka mataimakin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 12 ga watan Agustan 2023 da karfe 9 na safe a Makarantar ‘Yan Sanda da ke kan titin Maiduguri a Wudil.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.